George Weah zai karrama Wenger da babbar lambar yabo
Daga Aliyu Mustapha
Shugaban kasar Liberia George Weah zai karrama tsohon kocinsa, Arsène Wenger, da lambar yabon da ta fi martaba a kasar.
Wenger ne ya sayi Shugaba Weah, wanda shi ne kadai dan Afirka da ya lashe kyautar Dan kwallon duniya, a shekarar 1988 lokacin yana kocin Monaco.
Wenger, wanda ya bar Arsenal bayan ya yi shekara 22 a matsayin koci, ya sayi ‘yan wasan Afirka da dama lokacin yana ganiyarsa.
George Weah ya yi ritaya daga buga kwallon kafa a 2003 inda ya tsunduma harkar siyasa. Ya lashe zaben da aka yi a Liberia a shekarar da ta wuce da gagarumar nasara.
Ministan watsa labaran Liberia Eugene Nagbe ya shaida wa BBC cewa ana sa ran Wenger zai isa Monrovia, babban birnin kasar ranar Asabar domin karbar lambar yabon.