Na yi nadamar fitowa a akasarin fina-finan da na yi

Na yi nadamar fitowa a akasarin fina-finan da na yi

— Adam Zango

 

Mun dauko makune daga  hirar da BBC ta yi da jarumin, a kwankin baya

Jarumin na Kannywood wanda har ila yau yana shirya fina-finai sannan yana rera waka, ya ce “na fara harkokin fim ne a Kano inda nake share-share da goge-goge a masana’antar kade-kade da ake kira ‘Landscope Studio’.”

Game da abin da ya sa ya shiga harkar fina-finai, Adam ya ce, “tsoron kada na zama dan jagaliyar siyasa ko kuma dan shaye-shaye ne ya sa na tsunduma harkar.”

Adam, wanda ake yi wa lakabi da ‘Usher’ wata inkiya da ta samo asali tun yana makarantar sakandare saboda iya rawa, ya fito a fina-finai fiye da 100, a inda kuma ya shirya wasu fiye da 20.

A fagen waka kuwa, jarumin yana da kundi guda shida kuma kowane kundi na dauke da wakoki 12, a inda wakarsa mai taken Gumbar Dutse ta zama bakandamiyarsa.

Adamu kamar yadda har ila yau wasu suke kiransa, ya ce a duk fina-finansa, ya fi son Ahlil Kitab saboda irin gudunmawar da ya bai wa addinin Musulunci a cikinsa, kamar yadda ya bayyana.

Sai dai kuma fim din da ya yi mai taken Gwaska ne ya fi kowanne kwao masa kudi, duk da cewa shi ma fim din ya ci fiye da naira miliyan bakwai kafin a kammala shi.

‘Ni ba dan luwadi ba ne’

Fitaccen jarumin ya ce a kullum yana kwana yana tashi da bakin cikin zargin da wasu suke yi masa na zama dan luwadi (neman maza).

Wannan ne ya sa a wani lokaci a baya jarumin ya dauki Alkur’ani ya rantse cewa bai taba neman wani namiji da lalata ba.

“Wannan abin yana hana ni barci, kai har ma na taba zuwa neman aure amma aka hana ni saboda haka,” in ji Zango.

Game da batun cewa dan wasan yana da girman kai, jarumin ya kare kansa “Idan kana maganar masoya kana maganar miliyoyin mutane, to ta ya ya zan gamsar da su?”

Daga nan ya nemi masoyansa su rika yi masa uzuri domin shi ma mutum ne kamar kowa, kamar yadda ya ce.

A karshe ya yi magana kan yadda ake cewa ‘yan wasan Hausa “kudi suke nema kawai”, inda ya ce “muna yin fina-finan da za su kawo mana kudi.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *