Nasarar Tottenham kan Man U, Babban sakone
Inji Kane.
Daga Aliyu Mustapha
A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Sky Sports, dan wasan da ya ci kwallo daya a lokacin da Spurs ta lallasa Manchester United da ci 3-0.
Ya ce: “Mun isar da babban sako ne mu zo nan kuma mu yi nasara kamar yadda muka yi – babban sako ne. Mun so mu fara wannan kakar da kafar dama kuma mun samu nasarori uku cikin wasanni uku. Mun fara da sa’a.”
Kane ya ce ‘yan kungiyarsa ta Tottenham ba su yi wasa da kyau ba kafin a tafi hutun rabin lokaci, amma kwallon da ya ci bayan an dawo daga hutun ta yi matukar taimaka wa kungiyar sosai.
Bayan Kane ya ci kwallon ne dai Lucas Maura ya zura kwallaye biyu a ragar Manchester United.
Wannan ya sa Tottenham ta zama ta biyu a teburin gasar Firimiya yayin da take da maki daya da Liverpool, wadda ke saman tebur, sai dai kulob din su Mohammed Salah ya fi ta yawan kwallaye