Su wa ye fitattu a Kannywood bana?
An fitar da jerin sunayen ‘yan wasa da fina-finan da za su iya samun lambar yabo ta Kannywood.
‘Yan wasa ukun da aka ware don bai wa daya daga cikinsu Gwarzon Dan Wasa a bana su ne Sadiq Sani Sadiq (saboda hazakar da ya nuna a fim din “Bayan Duhu”) da Adam A. Zango (saboda rawar da ya taka a “Gwaska”) da kuma Ali Nuhu (saboda basirar da ya nuna a “Nasibi”).
A bangaren kyautar Fitacciyar ‘Yar Wasa kuma, wadanda aka zabo su ne Jamila Umar, wacce aka fi sani da Jamila Nagudu (saboda ficen da ta yi a “Na Hauwa”) da Rahama Sadau (“Halalci”) da kuma Nafisa Abdullahi (“Baiwar Allah”).
Sauran wadanda aka bayar da sunayensu da suka cancanci samun kyauta su ne:
Dan Wasa Mai Rufa Baya: Lawan Ahmad (“Da’iman”), Sadik Ahmad (“Nasibi”), Ali Nuhu (“Rumfar Shehu”).
‘Yar Wasa Mai Rufa Baya: Ladidi Fagge (“Da’iman”), Fati Shu’uma (“Basma”), Fati Washa (“Hindu”)