Da kamar wuya APC tayi nasara a wasu jihohi da yawa

Da kamar wuya APC tayi nasara a wasu jihohi da yawa

-Murtala Nyako

Daga Madina Ibrahim

Tsohon Gwamnan jihar Adamawa, kuma mai fada aji cikin jam’iyyar APC a jihar , Admirl Murtalay Nyako yace jam’iyyar APC mai mulki zata fadi zabe a jihohi da dama a Nijeriya, saboda rashin adalci da ya saka mambobinta da dama yin fushi da ita.

Da yake zantawa da manema labarai bayan sauka a filin jirgi a Yola bayan ya dawo daga duba lafiyar sa a kasar waje, Nyako ya ce jam’iyyar APC ita ce wanda ada talaka yake ganin zata share masa hawaye amma yin burus da bukatun jama’a da kuma rashin yin sulhu tsakanin mambobinta da suka fusata, ya sanya bata da qima da farinjini wajen alumma .

Ya ce tunda jam’iyyar APC ta bar turbar adalci ta hanyar yin watsi da damuwar mambobinta, dole ta fuskanci matsala.

Ya kara da cewa matsalolin jam’iyyar APC sun samo tushe ne daga zabukan Shugabanni da ta yi a fadin kasar nan. Nyako ya ce rashin adalcin da mahukuntan APC suka nuna a zabukan sabbin Shugabannin ne ya fara kawo baraka a cikinta.

Tsohon gwamnan ya ce da jam’iyyar APC ta saurari shawarar dattijai yayin gudanar da zabukan, da ba zata shiga matsalolin da ta ke ciki ba yanzu.

Tsohon jigo a jam’iyyar, ya cigaba da cewar APC kullum kara ragargaje wa take yi kuma ga zabe na kara matsowa, lamarin da ya ce ko shakka babu zai shafi nasarar jam’iyyar a zabukan shekarar 2019.

Nyako, daya daga cikin manyan ‘yan siyasa masu farin jini da yawan mabiya a jihar Adamawa da yakin arewa maso gabas, ya ce rashin daukan shawarar da suka bawa jam’iyyar APC ne ya saka ta cikin halin da take ciki yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *