Sarkin Lafia Isa Mustapha Agwai ya rasu yana da shekaru 84
Daga Zubairu M Lawal
Alhaji Isa Mustapha Agwai I, sarkin Lafia kuma shugaban kungiyar sarakunan jihar Nasarawa ya mutu yana da shekaru 84 a duniya.
Alhaji Sule Abubakar, Ajiyan-Lafiya ya tabbatar da mutuwar babban sarkin ga manema labarai a ranar Alhamis, 10 ga watan Janairu, a Lafia, kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito.
A cewar babban jami’i a masarautar, sarkin ya rasu ne a ranar Alhamis, 10 ga watan Janairu, a asibitin koyarwa na Turkiya da ke Abuja bayan fama da rashin lafiya.
Yace an nada ma sarkin sarauta a ranar 28 ga watan Mayu, 1974, sannan kuma kwanakin baya yayi bikin cika shekaru 44 akan mulki.
Marigayin sarkin ya mutu ya bar mata uku da yara biyu mace da na miji.
.