Na Cancanta In Lashe Kowacce Irin Kyauta A Afirka -SALAH
Daga Ibrahim Lawal
Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Muhammad Salah, ya bayyana cewa ya cancanta da lashe kowacce irin kyauta a nahiyar Afirka duba da irin kokarin da yakeyi a kungiyarsa da kasarsa ta haihuwa.
Dan wasan na Liverpool ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2018 wanda hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afirka take bayarwa duk shekara kuma ‘yan wasa daban daban suka lashe a baya.
Wata Mujallar kwallon kafa ta Faransa ce ta fara bayar da wannan kyauta ta Ballon d’Or a Afrika shekaru da dama da suka shude kafin daga bisani ta mika ragama ga Hukumar CAF a tsakan-kanin shekarun 1990.
Dan wasan tawagar Masar ya yi nasara ne a kan takwaransa Sadio Mane na Liverpool dan wasan tawagar kasar Senegal da Pierre-Emerick Aubameyang na Gabon mai wasa a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Arsenal.
“Na cancanta in lashe kowacce kyauta yanzu a nahiyar Afirka saboda kungiya ta tana kokari wato Liverpool sannan kuma kasar Masar taje gasar cin kofin duniya duk da cewa bamuyi kokari ba sai dai yanzu ina fatan lashe kofin Afirka” in ji Salah, wanda tsohon dan wasan Chelsea ne.
An gudanar da bikin karrama ‘yan wasan Afirka da suka yi fice ne a 2018 a fagen tamaula a babban birnin kasar Senegal kuma Muhammad Salah shi ne ya lashe kyautar 2017 da aka yi a Ghana.
Ragowar kyautukan da aka lashe sune:
Macen da babu kamarta: Chrestinah Thembi Kgatlana ta Afirka ta Kudu.
Matashin dan wasa: Achraf Hakimi mai taka leda a Borussia Dortmund dan kasar Morocco.
Kocin tawagar kwallon kafa ta maza: Herbe Renard mai horar da Morocco.
Koci mace mai horar da tawagar mata : Desiree Ellis ta Afirka ta Kudu.
Tawagar kwallon kafa ta mata: Tawagar Nigeria ta Super Falcons.
Tawagar kwallon kafa ta maza: Tawagar Mauritania.