Masu Zanga zanga suna kalubalantar Limamai a masallatai a Sudan
Daga Zubairu M Lawal
A kasar Sudan jami’an tsaro ne suka taimakawa wani fitaccen malamin addinin musulunci ficewa daga masallacin juma’a, sakamakon masu zanga-zanga da sukai kokarin far masa matukar bai jagoranci boren da suke yi kan tsadar Biredi da bukatar shugaba Omar el-Bashir sauka daga mukami.
A wani hoton bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta, an nuna wani mutum ya na yi wa Imam Abdul Hai Yusuf da ake zargin ya na goyon bayan gwamnati ihu tare da bukatar da tashi an jagorantar masu zanga-zangar.
Hatsaniya ta kaure ne a daidai lokacin da daya daga cikin masallata sallar juma’a a babban masallacin da ke al-Halfaya Bahri a arewacin Sudan, a lokacin da ya tashi ya na kalubalantar Imam Abdul Hai Yusuf saboda tun fara boren ‘yan kasar kan tsadar Burodi da sauran kayan bukatar yau da kullum.
Karanta wannan Labarin . Dubban Mutani sunyi Zamzan darshen a Ofishin Jakadancin Amurka sunce a Saki Sheikh Zakzaky.
‘Yan sanda dai sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar da suka yamutsa masallacin juma’ar da rera waken ki jinin gwamnati da kokarin tilastawa Imam Abdoul Hai Yusuf ya jagoranci boren na jiya juma’a.
Baya ga birnin Khartoum, lamari irin hakan ya kuma faru a wani masallacin juma’a da ke Sayed Abdel Rahman a birnin Khartoumbirnin Omdurman. Jami’an tsaro sun ce babu wanda ya rasa ran shi sai dai jikkata.
A baya dai malamin addinin musuluncin ya yi ficewa wajen yin Kudba a duk ranar juma’a kan halin da al’umar Syria da Falasdinawa ke ciki.
A wasu lokutan kuma ya sha jagorantar zanga-zanga da yin Allawadai kan kisan wadanda ba su ji ba ba su gani ba a Syria, da nuna kin amincewa da bude ofishin diflomasiyyar Amirka a birnin Kudus.
Tun ranar 19 ga watan Disambar bara ne aka fara bore a kasar Sudan kan tsadar burodi da man fetur. Daga bisani ya rikide zanga-zangar tilastawa shugaba Omar el-Bashir sauka daga mukamin da ya ke kai tun bayan juyin mulkin shekarar 1989.
Tattalin arzikin kasar ya shiga garari tun bayan ballewar Sudan ta Kudu a shekara 2011, saboda rasa kusan kashi 2 cikin 3 na man fetur da kasar ke da shi.
Ga kuma takunkumin da kasar ta yi fama da shi na shekara 20, ko da yake an janye ma ta a shekarar da ta gabata.