Atiku ya lashi takobin hana APC tafka magudi a zaben 2019

Atiku ya lashi takobin hana APC tafka magudi a zaben 2019

Daga Madina Ibrahim

Alhaji Atiku Abubakar, ya ce PDP zata dauki duk wasu matakai da ya dace don dakile jam’iyya mai mulki ta APC daga tafka magudi a zabe mai zuwa

Dan takarar Shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce jam’iyyarsa zata dauki duk wasu matakai da ya dace don dakile jam’iyya mai mulki ta APC daga tafka magudi a zaben Shugaban kasa na watan Fabreru, 2019 da ke gabatowa.

Da yake jawabi ga dandazon jama’ar da suka taru a gangamin yakin niman zabensa a Jos, Atiku ya ce tuni APC ta yanke shawarar tafka magudi kuma wannan ne ma dalilin da ya sanya basa yin kamfen na zabe a fadin kasar kamar yadda PDP take yi.

Ya ce PDP zata tabbata ta kawo karshen rikici da ta’ddancin da ake yi a jihar Filato da zaran an zabeta, kana ya bukaci daukacin masu kada kuri’arsu a jihar dasu zabi dan takarar jam’iyyar, Sanata Jeremiah T. Useni a matsayin Gwamnan jihar.

A cewar APC, ta haddasa asarar guraben ayyukan mutane da dama sakamakon wani mummunan tsarin tattalin arziki da ta dauka, kuma PDP zata wanke duk wani datti da APC ta kawo tare da samar da ayyukanyi, ma damar aka zabeta.

A jawabinsa, Shugaban majalisar dattijai, Sanata Abubakar Bukola Saraki, ya ce tuni APC ta haddasa wani rikici da kuma karya dokoki inda har ta samu nasarar raba kawunan majalisar tarayya, yana mai cewa ci gaba da gallazawa da tsare Sanata Dino Melaye na daga cikin yunkurin gwamnatin na rufe bakin ‘yan majalisun tarayyar.

Shima da yake jawabi, Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Uche Secondus, ya ce ba zasu lamunci ta’addanci a zabe mai zuwa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *