Man City ba za ta sayi dan wasa ba a Janairu’

‘City ba za ta sayi dan wasa ba a Janairu’

Daga Ibrahim Lawal

A ranar Litinin ne Manchester City za ta kara da Wolverhampton Wanderers a karashen wasan mako na 22 a gasar Premier A Ettihad.

City tana ta biyu a kan teburin Premier da maki 50 da tazarar maki bakwai tsakaninta da Liverpool ta daya, wadda ta buga karawa ta 22 a ranar Asabar.

Liverpool ta yi nasarar cin Brighton daya mai ban haushi, kuma Mohamed Salah ne ya ci kwallon a bugun fenariti.

Pep Gaurdiola ya ce ba za su sayo dan kwallo ba a watan nan na Janairu, sai idan ta kama za su iya dauka aro na karamin lokaci.

Kocin ya kara da cewar a irin wannan lokacin ba za ka samu dan wasa mai kwari ba, domin kowacce kungiya ba ta son rabuwa da manyan ‘yan kwallonta domin kakar wasa ta yi nisa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *