An kai hari kan asibiti a birnin Khartoum ta Sudan

An kai hari kan asibiti a birnin Khartoum ta Sudan

Daga Ibrahim Lawal

Wata kungiyar likitoci a Sudan ta ce jami’an tsaron kasar sun harba hayaki mai sa hawaye cikin harabar wani asibiti.

Kungiyar ta kuma ce an kama wasu ma’aikatan jinya a daidai lokacin da dubban masu zanga-zanga suka shig titunan Khartoum babban birnin kasar.

Ana yin irin wannan zanga-zanga a dukkan sassan kasar, kuma hukumomi sun ce an kashe mutum 24 bayan mutum 800 da aka kama tun bayan da boren ya fara a watan jiya.

‘Yan sanda sun shafe sa’o’i suna harba hayaki mai sa hawaye, kuma jami’an tsaro na cikin gida sun rika kora dubban masu zanga-zanga a ynkin Bahri da ke kudancin Khartoum.

Kungiyar likitocin Sudan ta ce an harba hayaki mai sa hawaye da harsasai a cikin wani asibitin yankin.

Kungiyar wadda ta dade tana sukar gwamnatin Sudan ta yi kira da a saki likitoci fiye da 12 da aka kama a lokacin boren.

Matsalar tattalin arziki ce ta janyo wannan zanga zangar a fadin kasar, kuma wannan ne kalubale mai girma ga Shugaba Omar Al-Bashir wanda ya shafe shekara 30 yana mulkin kasar.

Ana tsare da mutum fiye da 800 kuma kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun ce jami’an tsaro sun kashe a kalla mutum 40.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *