Hatsarin jirgi ya kashe mutum 15 a Iran

Hatsarin jirgi ya kashe mutum 15 a Iran

Daga Madina Ibrahim

Wani jirgin daukar kaya ya yi hatsari kusa da birnin Tehran babban birnin Iran, inda mutane 15 suka mutu a kokarin da yake yi na sauka a lokacin da ya fuskanci rashin kyawun yanayi.

Jirgin dai mai kirar 707 ya kauce ne daga titin jirgi inda ya bugi bango a daidai lokacin da yake kokarin sauka a filin jirgin Fath da ke Karaj, kilomita 40 daga yammacin Tehran.

Sojojin kasar sun bayyana cewa mutum daya wanda shi ne injiniyan jirgin ne kawai ya rayu cikin mutane 16 da suke cikin jirgin.

Jirgin dai ya yi hatsari ne a daidai lokacin da yake dakon nama daga Bishek, babban birnin kasar Kyrgyzstan.

Har yanzu dai babu wani karin bayani a kan wanda ya mallaki jirgin.

Sai dai wani mai magana da yawun hukumar sufuri ta Iran din ya bayyana cewa jirgin na Kyrgyzstan ne, amma a wani bangaren kuma an bayyana cewa jirgin na kamfanin jirgin Payam ne da ke Iran.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *