Kungiyar Izala ba ta siyasa bace

Kungiyar Izala ba ta siyasa bace – Sheikh Gumi

Daga Zubairu M Lawal

Daya daga cikin malaman kungiyar Izala a Najeriya, Dakta Ahmad Mahmud Gumi ya ce kowane dan kungiyar na da ikon ya zabi gwanin sa inda maslahar sa take domin kungiyar Izala ba ta siyasa bace.

Dakta Gumi ya bayyana hakan ne a cikin daya daga karatuttukan da yake gabatarwa a masallacin sultan Bello, garin Kaduna a ranar Asabar 12/01/2019 inda ya ja hankalin dukkan Ahlussunnah akan kada su bari wasu mutane su yaudare su da cewar ga wanda zasu zaba.

“Kowa ya duba inda maslahar duniyar sa take ya zabi wanda ya ke so. Kada ku bari wasu fake da wata gararinsu su ce ku zabi wani. Ku duba halayen da zasu iya daidaita wannan kasa da al’ummar ta.

“Aikin izala ba na siyasa ba ce, aikin tabbatar da sunnah ne. Malam Abubakar Mahmud Gumi ya bar wannan kungiyar a hannun wasu dattijai. Son zuciya ne kawai ya hana kungiyar ta hadu. In Sha Allah nan ba da jimawa ba kungiyar zata dawo kan turbarta aka daura ta.” Inji shi.

Daga karshe kuma ya ya ce kungiyoyin Izala da Darika su ji tsoron Allah kada su bari fitinar da ta samu shi’a ta same su inda yace su ba zasu bari a bata wannan kungiya ba saboda ikhlasin wanda suka kafata.

3 Replies to “Kungiyar Izala ba ta siyasa bace”

  1. Wannan bayani yayikyau, Allah yasakawa malam da alkhairi. Ameen.
    Kuma yakamata malamai da AlmJirai sufahimci wannan bayanin da idon baseera, da fahimta da zuciya me kyau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *