Zaiyuhu kuwa? An dage shari’ar Alkalin Alkalan Najeriya
Daga Aliyu Mustapha
Kotun da’ar ma’aikata ta dage zamanta na sauraron shari’ar da ake wa Alkalin Alkalan Najeriya Mai shari’a Walter Onnoghen, bayan ya ki bayyana a gaban kotun a ranar Litinin.
Laifuka shida ne ake tuhumar babban alkalin, dukkanninsu sun shafi kin bayyana dukiyar da ya mallaka.
Sai dai babban alkalin ya tura wasu manyan lauyoyi 47 wadanda suka wakilce shi.
Lauyoyin babban alkalin sun ce bai bayyana ba ne saboda ba a mika wa mutumin da suke karewa takardar sammaci a hannunsa ba.
Abin da ya sa kotun dage zamanta har zuwa ranar Talata 22 ga watan Janairun.
Bayan an kwashe lokaci ana gardama tsakanin lauyoyin da ke kare Mista Onnoghen da wadanda ke kara kan ko wajibi sai wanda ake kara ya bayyana a gaban kotun.
Sai Alkalin kotun Danladi Umar, ya ce dole sai ya bayyana a gaban kotun da kansa, kafin a fara sauraron karar.
Ko da yake lauyoyinsa sun ce kotun ba ta da hurumin sauraron karar. Sun ce ba a bi ka’ida ba wajen gurfanar da shi.
Ana sa ran kotun za ta tube shi daga mukaminsa domin kada ya yi katsalandan ga shari’ar.
Gwamnatin tarayya dai na zarginsa ne da saba wa dokar kotun da’ar ma’aikata ta Code of Conduct Bureau.
Rahotanni sun ce tun a ranar Juma’a aka sanar da shi kan lafiukan da ake zarginsa da kuma bukatar ya gurfana gaban kotu a ranar Litinin.
A ranar 10 ga watan Nuwamban 2016 ne Shugaba Muhammadu Buhari ya rantsar da Walter Onnoghen a matsayin alkalin alkalai na riko kafin tabbatar da shi.
Wannan dai zai kasance shi ne karon farko da alkalin alkalan Najeriya zai gurfana gaban kotu kan zarginsa da aikata laifi.
A 2015 ne dai alkalin kotun da’ar ma’aikata mai shari’a Danladi Umar wanda ya jagoranci shari’ar mai sharia Onnoghen, ya yi watsi da tuhume-tuhume kan shugaban Majalisa dattawa Bukola Saraki kan zargin karya wajen bayyana kadarorinsa.