2019 Zaben Buhari da Atiku zai wargaza Kungiyar Izala
Daga Aliyu Mustapha
A karshen makon jiya ne Kungiyar Izala a Najeriya ta bukaci mabiyanta da su zabi Shugaba Muhammadu Buhari, amma wani jigo a kungiyar Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun ya ce shi Atiku zai zaba.
Sabanin matakin da kungiyar ta dauka, Sheikh Rigachikun ya bayyana alkiblarsa karara cewa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ne zabinsa a 2019. Saboda “yadda yake yi wa addini hidima,” a cewarsa.
Sai dai Shugaban kungiyar na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya ce sun yanke shawarar mara wa Shugaba Buhari baya ne bayan wani taro na kasa da suka gudanar.
Ya ce sun lura yadda ake fuskantar lokacin zabe mawuyaci, “ya kamata a yi saitin al’ummar Musulmi kan abin da ya kamata.
Har ila yau, akwai Sheikh Ahmad Gumi wanda ya kwashe lokaci mai tsawo yana sukar manufofin Shugaba Buhari.
Kuma a lokuta da dama cikin karatunsa yana bayyana rashin goyon bayansa ga takarar Shugaba Buhari a 2019.
Sai dai bai fito karara ya ce a zabi Atiku Abubakar a zaben 2019.
Amma kuma yana cikin mutanen da suka sulhunta Atikun da tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo wanda ya yi aiki a karkashinsa.
Abin da ya kara karfafa zargin da ake wa malamin cewa yana goyon bayan takarar Atiku.
A daya bangaren kuma akwai Sheikh Kabir Gombe wanda shi ne sakataren kungiyar Izala wanda kuma shi ma wadansu suke ganin ya fi karkata ga Shugaba Buhari.
Kamar yadda ake ganin kawunan malaman Izalan ya rabu, kamar yadda ‘yan takarar shugabancin kasar suka raba kan masu shirya fina-finan Hausa.
Wani bangare yana goyon bayan Shugaba Buhari, yayin da guda kuma yake tare da Atiku Abubakar.
Har ila yau, akwai wasu malaman Izala da ke tsakiya, wato ba su nuna goyon bayansu ga kowane dan takarar a fili ba.
Magoya bayan Buhari sun ce ya taka rawar gani, sai dai magoya bayan Atiku sun ce akwai bukatar canji a kasar.
Da alama zaben 2019 zai fi wadanda suka gabace shi ta fuskar rabuwar kawunan al’umma da ke mara wa mabambantan ‘yan takara baya.
Wasu masu sharhi kan al’amura a kasar suna ganin hakan bai rasa nasaba da yadda duka manyan ‘yan takarar biyu sun fito ne daga yanki guda – wato arewacin kasar