An tsayar da ranar wasan Real da Barca
Daga Ibrahim Lawal
Mahukun gasar La Liga sun tsayar da ranar da za a buga wasan hamayya na El Clasico na biyu tsakanin Real Madrid da Barcelona wato El Clasico.
Shugaban hukumar gasar, Javier Tebas ya tabbatar cewar kungiyoyin biyu za su fafata ne a ranar 2 ga watan Maris a Santiago Bernabeau.
Barcelona ta karbi bakuncin Real a wasan farko a La Ligar bana, inda ta doke Madrid da ci 5-1 a ranar 28 ga watan Oktoba a Nou Camp.
‘Yan wasan da suka ci wa Barca kwallayen sun hada da Philippe Coutinho da Arturo Vidal da Luis Suarez wanda ya zura uku a raga, yayin da Marcelo ya ci wa Madrid daya.
Bayan karawar ce Real ta sallami kocinta Julen Lopeteguita kuma ta sanar da nada Santiago Solari a matsayin rikon kwarya a ranar 29 ga watan Oktoba, 2018.
Bayan da aka buga wasan mako na 19 a La Ligar bana, Barcelona tana mataki na daya a kan teburin da maki 43, ita kuwa Real Madrid tana ta hudu da maki 33.