Da Dumi Duminsa- Meyasa Atiku ya riga Buhari shiga dakin taron muhawarar ‘yan takarar shugaban kasa ?
Daga Aliyu Mustapha
A daren yaune ake gudanar da muhawarar yan Takarar Shugabancin kasa tsakanin yan Takarar Jam’iyyu dabam dabam Labarin da muka samu yanzu na nuni da cewa dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya isa dakin da ake gudanar da taron muhawarar da aka shiryawa ‘yan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyun siyasar kasar.
Atiku Abubakar ya halarci dakin taron ne bayan kusan awa daya da fara taron, wanda kuma hakan ya sa ya riga dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC, Muhammadu Buhari isa dakin taron.
Rahotanni dai na nuni da cewa da kamar wuya shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu damar halartar taron.
Wannan kuwa ba zai iya rasa nasaba da gajiyar da shugaban kasar yayi ba, bayan da ya kaddamar da babbar tashar jiragen ruwa ta Baro a jihar Niger, da kuma kaddamar da yakin zabensa a garin Jos, jihar Filato, duka a ranar Asabar.
Sai dai da yawa na ganin hakan ba zai zama hujja ga shugaban kasar na kin halartarshi taron ba, kasancewar shima Atiku Abubakar, ya dawo kasar Nigeria ne bayan ziyarar kwana biyu da yakai kasar Amurka, inda kuma bai nuna gajiyar halartar taron ba.
Atiku Abubakar, a shafinsa na Twitter, ya ce gazawar shugaban kasa Buhari na halarta taron babban cin fuskane ga demokaradiyyar Nigeria, inda kuma ya ce ba zai iya kalubalantar Buhari ba kasancewar baya wajen.