Kotu Ta Bada Belin Dino Melaye
Daga Aliyu Mustapha
Wata babbar kotu mai zama a Maitama, Abuja, ta bada belin sanata Dino Melaye yau Jumma’a, kotun ta bada belin a cewarta don Melayen ya je neman magani,
Melayen wanda yake tsare a hannun jami’an ‘yan sanda tun ranar 4 ga watan Junairun nan, ya shigar da kara ne a gaban kotun don ta bi mishi kadin shi. Mai shari’a Yusuf Halilu ne ya bada belin Melaye din, bayan da lauyan da yake wakiltar Melaye,
Cif Mike Ozekhome(SAN) ya sigar da kara gaban kotun, mai shari’an y ace duk da cewar ba a shigar da kara a gaban kotun ba, amma zai bada belin Dino don ya je neman magani. Kotun ta gindaya wasu sharudda kafin ta bada belin Dinon, daga cikin sharuddan sun hada da kawo mutum uku da zasu tsaya wa Dino din, sai kuma biyu daga cikin mutanen dole ya zama suna da kaddara a cikin garin Abuja, an dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga watan Junairu.