Rashin kula da kan iyaka yasanya miyagun mutani ke shiga Nijeriya
Inji Mister Brigitte Eno
Daga Zubairu .M.Lawal
Majalisar dinkin Duniya za su taimaka ma Najeriya wurin rage
kwararowar bakin Haure.
Jakadun Najeriyan dai sun kara wata ganawa ta biyu ne da wakilan
Majalisar Dinkin Duniya masu kula da yan gudun hijira dan magance
wannan matsala ta bakin haure.
Da take magana wakiliyan Majalisar Xinkin Duniya kuma mataimakiyan
Shugaban hukumara kula da yan gudun hijira ta majalisar Xinkin Duniya
dake vangaren hukumar kungiyar kawancen Afirka Misis Brigitte
Mukanga-Eno tace; ya zama wajibi hukumomi da masu fada aji na Nijeriya
su miqe tsaye wajen kulawa da kan’iyakokin qasashen da suka hada da
Nijeriya saboda barin mutani kowani iri na shigowa yakan janyo vata
gari na samun damar shiga qasar suna aikata ayyukan Ta’addanci.
Tace; Majalisar Xinkin Duniya zata taimakawa Nijeriya wajen dakile
shigowar vakin haure masu shigowa da sunan yan gudun hijira.
Tace; akasarin vatagari suna daukar wanan hanyar ce ta zama mafi sauki
su shigo qasashe suna ta’addanci.
Ta kara da cewa tun a watan Nawambar bara Majalisar Xinkin Duniya ta
buqaci Gwamnatin Nijeriya da ta tabbatar hukumar kula da kan iyakokin
qasarta sun sanya ido sosai akan Bodojin dake Jihohin da suke da iyaka
da wasu qasashe.
Itama a nata jawabin Babban hadimar Gwamnatin Nijeriya dake kula da
Sansanonin gudun hijira Malama Sadiya Faruk tace; wanan shawarar abin
dubawane kuma abin ayi amfani da shine.
Saboda a wasu lokutan mutani na tururuwa zuwa sansanonin yan gudun
hijira ba tare da ansan daga ina suke ba . Amma suna amfani da sunan
yan gudun hijira harma wasu lokutan kaga an tarar da abubuwan cutar da
alumma a sansanin ko kuma akai hare haren Ta’addanci a sansanin yan
gudun hijira.
Tace; yana da gayar mahimmanci ga Nijeriya a matsayinta ta Babban qasa
tayi amfani da Bodojinta wajen kariya ga alumman qasan ta.
Taron na masu ruwa da tsaki ya maida hankali kan yadda itama kungiyar
Tarayyar Afirika zatayi am fani da jami’an tsaronta na kan iyakokin
qasa da qasa wajen dakile ire iren wadanan mutani.