Arsene Wenger kadai zai magance matsalar da muke ciki
Inji Bayern Munich
Ibrahim Lawal
Rahotanni daga kasar Jamus sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich zata iya daukar tsohon kociyan Arsenal, mista Arsene Wenger sakamakon rashin samun nasara da kungiyar take ciki ta hannun kociyan kungiyar Nico Kobac.
Kobac ya zama kociyan kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen ne a farkon wannan kakar bayan kungiyar ta rabu da kociyanta kuma har yanzu basu gamsu da salon da kungiyar take buga wasa ba.
Bayern Munchen dai ta buga wasanni hudu bata samu nasara ba a shekarar data gabata kuma kungiyar ta buga wasanni biyu a jere a gasar Bundes Liga ba tare data samu nasara ba hakan ya sa a ka fara tunanin kungiyar zata iya rabuwa da kociyan nata.
Rahotanni na baya bayan nan dai sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen bata niyyar korar kociyan nata amma kuma rahoto ya tabbatar da cewa kungiyar ta kirawo taron ‘yan jaridu akan rikicin kungiyar da kuma yiwuwar kawo Wenger. Shugaban kungiyar Uli Hoeness da daraktan wasannin kungiyar Kerlz Rummenigge da kuma mai kula da harkokin kwallon kafa na kungiyar Hassan Salihamidzic zasu hadu domin tattaunawa akan makomar kungiyar da kociyan.
Tuni dai rahotanni suka fara bayyana cewa tsohon kociyan Arsenal mista Arsene Wenger ne zai maye gurbin kociyan kungiyar idan har an koreshi duk da cewa kawo yanzu anyi rabi a gasar ta Bundes Liga da gasar cin kofin zakarun turai.