shege ka fasa – Dakarun Sojan sama sun isa birnin Sokoto

 

Dakarun Sojan sama sun isa birnin Sokoto

Daga Zubairu m Lawal

Rundunar sojin sama ta Nijeriya ta tura dakarunta da jirgin yaki tare da makamai zuwa jihar Sakkwato domin yaki da ‘yan fashi da masu garkuwa mutane. Kakakin rundunar sojin sama Ibikunle Daramola ce ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta baiwa manema labarai, ta ce an tura dakarun ne tare da jirgin yaki domin taimakawa rundunar Operation Diran Mikiya da ke yaki da ‘yan bindiga tsakanin kan iyakar jihohin Sakkwato, Zamfara da Katsina. Tuni sojojin suka isa Sokoto a ranar Lahadi domin soma yaki da ‘yan fashi da suka addabi yankin na arewa maso yammacin Nijeriya.

Babban kwamandan sojin sama a Sakkwato Air Vice Marshal Oladayo Amao da ya tarbi sojojin, ya bukaci su nuna kwarewa ga aikin da aka turo su na tabbatar da tsaron al’umma da kuma yakar ‘yan fashi.

Sanarwar ta kuma ce za a inganta filin jirgin Sultan Abubakar III a Sakkwato da dukkanin abubuwan da suka wajaba domin kaddamar da hari ta sama daga

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *