Arsenal ta na Son Gareth Bale
Daga Ibrahim Lawal
Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta fara tattaunwa da wakilin Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Gareth Bale domin ganin Dan wasa yakoma Arsenal a kakar wasa mai zuwa.
Arsenal dai ta dade tana neman Dan wasan mai shekaru 29 a duniya wanda take ganin zai taimaka mata wajen kara karfi a gasar firmiya dana zakarun turai kuma sannan zai maye mata gurbin Mesut Ozil wanda kociyan kungiyar yake son siyarwa.
Ba’a Haifi Wanda Zai Maye Gurbin Ronaldo Ba
Arsenal da Real Madrid da Barcelona ke zawarcinshi ?
Yawan jin ciwo yasa kungiyar tayi sanyi da neman Dan wasan Dan asalin kasar wales wanda yakoma Real Madrid daga kungiyar kwallon kafa ta Tottenham akan kuDi fam miliyan 83 a shekara ta 2013 kuma tun bayan komawarsa yake taimakawa Real Madrid wajen lashe kofuna.
Bale dai ya buga wasanni goma ne kawai a wannan kakar tsakanin kungiyarsa ReL Mdrid da kasarsa ta Wales sakamakon yawan jin ciwo da yakeyi kuma da alama Dan wasan ya buga wasansa na karshe a wannan watan bayan yasake jin rauni a satin daya gabata a filin Daukar horo a kungiyarsa ta Real Madrid.
Sai dai duk da yawan ciwon da Dan wasan yake hakan bai hana Arsenal neman Dan wasan ba inda ta shirya tsaf domin neman Dan wasan a kakar wasa mai zuwa idan Dan wasa Ozil yabar kungiyar kamar yadda suka tsara.
Real Madrid dai ta yiwa Dan wasan kuDi fam miliyan 85 a kwanakin baya sai dai a ‘yan kwanakin nan rahotanni sun bayyana cewa Madrid Din ta rage farashin Dan wasan zuwa fam miliyan 62 domin samun mai siya. A kakar wasan data gabata dai Dan wasan ya zura kwallaye 12 ne kawai cikin wasanni 32 daya buga gaba Daya daya buga daga Real Madrid har Wales sai dai ya zura kwallo a wasan karshe na kofin zakarun turai da suka doke Liberpool daci 3-1.