Babban magana: ko Amaechi zai bar APC bayan ya kushe Buhari ya yabawa mai gidansa
Daga Aliyu Mustapha
A wani fai-fai na murya inda aka ji ministan shugaban kasa Muhammadu Buhari yana yabawa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a matsayin mai kishin kasa.
Anji muryan minister yana cewa Obasanjo mutum ne mai kishin kasa duk da cewa ana zargin sa da wawurar dukiyar Najeriya.
wannan fai-fai da aka saki ba da jimawa ba, an ji Amaechi yana cewa ko da mutum ba ya son Obasanjo, ya san cewa shugaba ne wanda bai nuna
kabila na fifita ‘yan uwan sa yarbawa ko kuma mutanen yankin sa.
Idan ba a manta ba kwanaki baya ne Fasto Omokri wanda yayi aiki da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, shi ne ya saki fai-fen da aka ji Mista Rotimi Amaechi yana caccakar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Wannan karo, Reno Omokri, ya kuma sakin wani fai-fai na 6 a jerin da ya kira AmaechiTapes.
Babban Ministan sufurin kasar ya kara jaddada cewa zai yi wahala a iya canza Najeriya domin kuwa mutanen kasar musamman Talakawa matsorata ne da ba za su iya yin fito-na-fito na ganin an yi wani juyin juya hali ba.
A fai-fen da aka saki a farko an ji yadda ministan na Najeriya yake nuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari mutum ne maras jin shawara, mai dan-karen taurin kai kuma wanda ba ya karatun damuwar alumma masamman mawuyacin halin da ake ciki yanzu.