KOWA YACI LADAN KUTURU : Bala Lau ya samu alfarma daga wani Gwamnan APC
Daga Madina Ibrahim
A makon da ya gabata ne shugaban kungiyar Izala ta kasa (JIBWIS), Sheikh Bala Lau, ya shelanta matsayin Kungiyarsu akan babban zabe mai zuwa ida yace sun amince kungiyar Izala zata zabe Shugaban kasa Muhammad Buhari ya kuma bukaci mambobi da magoya bayan kungiyarda su zabi shugaba Buhari a zabe mai zuwa
Duk da cewa a wananan makon labarin ya tada kura saboda wasu jiga jigan Malaman Kungiyar Izala sunce bada yahunsu ba . sun ware cewa Atiku yafi cancanta saboda yana taimakon jama’an kasa kuma ya gina masallatai sama da 100.
Bayan furucin na shugabannin kungiyar ta Izala wanda ya farantawa APC rai , rahotanni su ka bayyana cewar gwamnan jihar Kaduna ya bawa Sheikh Lau kyautar wasu motocin alfarma aka kuma nuno motochin.
Sai dai a wani jawabi da kungiyar Izala ta fitar, Sheikh Bala Lau, ya karyata rahotannin da ke cewar an bashi kyautar mota
Shugaban kungiyar Izala ta kasa (JIBWIS), Sheikh Bala Lau, ya kalubalanci gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El_Rufa’i, da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da su fito su bayyana lokacin da su ka bashi kyautar mota.
Sai dai Rohotanni sun bayyana cewa Malamin Babban na hannun damar Shugaban kasane da Gwamnan jihar Kaduna koma menene zai iya faruwa .
Saboda a lokacinda Gwamnatin jihar Kaduna ta haranta harkokin YAN Shi’a a Kaduna shine ya fito ya jaddada a kafafen yadda labarai .
Shiyasanya ma lokacin da Sheikh Bala Lau yace sun bayyana goyon bayansu na zaben Buhari wasu ke cewa bai kamata malamai na shiga harkan YAN siyasa ba .
A makon da ya gabata ne shugaban kungiyar ta Izala ya nemi mambobinsu da magoya baya da su kada kuri’un su ga shugaba Buhari a zabe mai zuwa.
Sai dai, bayan Sheikh Lau ya yi wannan furuci ne rahotanni su ka bayyana cewar El-Rufa’i ya bahi kyautar motoci saboda yiwa Buhari kamfen.
Da yake kare kansa a kan wannan zargi, Sheikh Lau ya ce zancen, zuki ta malle ce kawai tare da fadin cewar, “kowa ya yi da kyau ya sani .”