Shekaru 40 da fara Gwagwarmaya ko kunsan Manufar Shaikh Zakzaky ?
Daga wakilinmu
Ya zuwa yanzu Da’awar da Shehin Malamin nan mai kira a komai ga tsarin Allah, ma’ana mutum ya rika yiwa kansa hisabi ya tsare kansa daga laifin da zai kasa kare kansa a lahiri .
Shaikh Ibraheem Zakzaky wanda a yanzu haka yake tsare a hannun Gwamnatin Nijeriya kusan shekaru uku batare da an barshi yaje ya nime Lafiyan jikinsaba duk da cewa akwai manyan raunuka a tattare dashi da Matarsa Malama Zinatuddin Ibraheem.
mabiyarsa sunyi bukin gudanar da taruruka na tunawa daga ranar da Shiakh ya fara shelanta wannan kirara bainar jama’a . wanda yanzu ya cika shekara 40 da fara wanan Gwagwarmayya.
Wakilinmu ya nakalto mana hadafin dake cikin wanan Gwagwarmayyan na Shaikh Zakzaky Wanda
Malam Saifullahi M. Kabir ya rubuta a shafinsa
A sha karatu Lafiya
A wani tattaunawarsa da wani dalibin jami’ar Ahmadu Bello, bangaren ilimin siyasa, a ranar 27/8/2003, Jagoran Harka Islamiyyah a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayyana cewa: “Mu muna kiran kanmu ISLAMIC MOVEMENT ne, shine mu. Ba wanda mutanen gari suke kiranmu ba, (wato ba wasu sunayen da mutanen gari ke kiranmu ba).”
Shaikh Zakzaky ya kara da cewa: “Ita kuma Islamic Movement (Wato Harkar Musulunci) ba Kungiya ce mai ‘register’ kamar sauran kungiyoyi da ka sani ba, ba ‘formal Organization’ bace, ‘Idea’ ne na wasu mutane da suke hankoron su ga sun cimma wani buri na ganin an tabbatar da addini, ya zama cewa addinin Musulunci yana iko da kasa.”
Ya kara da cewa: “Duk wanda yake da ra’ayi na cewa da za a tambaye shi, meye kake tunanin ya zama makomar Nijeriya, yana ganin makomarta ya zama Musulunci ne, kuma yana hankoron hakan, yana yunkurin hakan ta wadansu ayyuka, to ‘naturally’ (a dabi’ance) ya zama dan Islamic Movement ko yana tare da mu ko baya tare da mu, in dai yana wasu abu don hankoron cimma wannan manufar.”
Malam Zakzaky yace: “Kaga Islamic Movement ba sunan Organization bane, ‘Concept’ ne, wato kai dan Islamic Movement ne in har kana yin wani motsi don cimma wannan nufin na yunkurin dawowar addinin Musulunci ya yi iko.
Don haka akwai wadansu wadanda suke suna iya zama ‘yan Islamic Movement, amma ‘passive members’, suna da ra’ayin Harkar Musulunci din, amma ba su yin komai (na yunkurin ganin Musuluncin ya dawo ya yi iko).”
Shaikh Yace: “Kaga idan kana ‘sharing view’ din, (kana da ra’ayin Addinin Musulunci ya dawo ya yi iko), to kamar kana Harkar ne, amma idan ya zama kana yunkurin aiwatar da hakan, za a iya ce maka ‘active member of the Islamic movement’.
Domin in kana da ra’ayin hakan amma baka yin komai, tamkar kaima dan Harkar ne ta wani janibi. Akalla a tunaninka kai dan Harkar Musulunci ne, ko da baka yin komai (na motsi din da ake yi).
Don haka, mu ana iya ce mana ‘active members of the Islamic Movement’ saboda mu muna dan tagazawa ko yaya, ko da yake bai isa ba.”
“Shi Islamic Movement ‘concept’ ne, ba Kungiya bace, wanda duk yake da wannan ‘idea’ din kawai ma shi dan ‘Movement’ din ne. Don haka duk inda akwai Islamic Movement, bangare ne na Islamic Movement din Duniya.”
Ba tare da na tsawaita ba, daga wannan bayanin, mutum zai iya fahimtar mece ce ita wannan Harka ta Musulunci da yau ake bikin cikarta shekaru 40 da shelantawa.
Harka Islamiyyah tana da hadafi (manufa), da buri da kuma hanyoyin cimma wadannan hadafi da burika din. Wanda kila ba laifi idan muka dan waiwayi kowannensu a daidai nan wajen.
Manufa ko Hadafin Harka Islamiyyah:
Shaikh Zakzaky yana cewa: “Manufar Harkar Musulunci shine tabbatar da addinin Musulunci a rayuwarmu da kuma a cikin al’ummar da muka samu kanmu a ciki.
Wato a Nijeriya ko ma ba lallai a Nijeriya ba, a duk inda muka samu kanmu.
Domin mu muna ganin Nijeriya kanta ba bukatar samammen ketaren da turawa suka saka mana, saboda haka akwai Islamic Movement a Nijar, ba kuma ana ganin Islamic Movement din Nijer bace daban, duk iri daya ne, akwai a Cameroon, nan ma Islamic Movement iri daya ne, ba ta Kamaru bace daban. Wato ita wannan Harkar ta Musulunci tana Nijeriya ne da makwaftanta. ‘Idea’ din ya yadu a duk fadin Yammacin Afirka, ko da yake bai yi karfi kamar yadda yake a cikin Nijeriya ba.”
Malam (H) yace: “Da yawa mutane idan suka ji an ce ‘establishment of Islam’ (Kafa addinin Musulunci) su kan yi tunanin kafa ‘Islamic state’ da ‘islamic government’ (kasar Musulunci da gwamnatin Musulunci) ne kawai. Amma wannan mu a wajenmu kafuwar Musulunci a mutane ne a farko, Musulunci na fara kafuwa a kan mutane ne, idan mu a karan-kanmu addinin Musulunci ya zama shi ke gudanar da rayuwar mu, to daga nan ne za a kai ga (kafuwar) gwamnati da kuma kasar Musulunci.”
Shaikh Zakzaky yace: “Shi kafa gwamnatin Musulunci ko kasar Musulunci bangare ne (na kafuwar Musuluncin a daidaikun).” Don haka yake cewa: “Muna so ne Musulunci ya gudanar da rayuwarmu a kan kanmu da kuma a cikin al’ummar da muka samu kanmu.”
Sannan kuma ita Harka Islamiyyah din nan, bangare ce ta Harka Islamiyyah din Duniya baki daya. Kamar yadda Shaikh Zakzaky ke cewa: “Misali a Iran, ai gwagwarmayar Musulunci ne ta kafa gwamnatin Musulunci din.”
Wato Harka Islamiyyah a ko ina sunanta Harka Islamiyyah. Kuma wannan da ake yi a Nijeriya ko Afrika bangare ce na Harka Islamiyyah din Duniya, wacce ta faro tun daga zamanin Manzon Allah Muhammad (S).
Don haka ma mutum babban mahaukaci ne idan ya bude baki yace wai yai ka haramta Harka Islamiyyah din.
Burin Harka Islamiyyah:
A bayanan Malam (H) da ya gabata kun ji wani burin Harka Islamiyyah din, wato hadafi shine tabbatar da addinin Musulunci a kawukanmu.
Ya zama mu da muka amsa kiran mun siffantu da abin da Allah ke so, mun nesanci duk abin da baya so ko ya hane mu da aikata shi. In aka samu haka an cimma hadafi.
To kuma cimma wannan hadafin shi kai mu ga samun tabbatar da addinin a doron kasar da muke. Wanda wannan kuma muna iya ce masa burinmu.
A wani wa’azi da Shaikh Zakzaky ya yi ga al’umma a garin Katsina a shekarar 2013, ya bayyana cewa: “Ta yiwu mutum ya ce mana, to ai lallai dawo da addinin musulunci ba fa zai yiwu ba! Don akwai wanda suke ce min ba fa zai yiwu ba sam, saboda an riga anyi nisa!”
Shaikh Zakzaky yace: “Sai mu ce ma (mai wannan tunanin) hatta har in haka nan ne, ka ga idan muka tsaya muka ce a koma ga addinin musulunci, to za mu gamu da Allah gobe qiyama muna da uzuri.
Don za a ce me ya sa ku ka shantake a qasar da aka mayar da addinin musulunci tamkar laifi, ku ka yi zaman ku? Sai mu ce ya Rabbi, a yayin da muka ga ana haka nan, mun ce ma mutane a dawo ga addini, amma sai ba su saurare mu ba, sai suka fasa, suka qi yi. Kuma mun yi sa’a ma sun kashe mu, sai muka yi Shahada! To ka ga mun samu mafita.”
Idan mun fahimta sosai, manufar shine mu da muka amsa kiran ya zama mun mai da addini ya zama mu, mu zama addini din, sai mu cigaba da kiran saura zuwa ga hakan, in an kashe mu a kan wannan kiran kafin kafa daular addini, shikenan muna fatan ya zama mun samu uzuri a wajen Allah (T).
Idan kuma mun rayu har aka kafa daular addini din, to dai nasara a wajen kowanne dayanmu shine shi ya koma ga Allah yana mai yarda da shi.
Wato rashin kafa gwamnatin Musulunci ba rashin nasarar wannan Harkar bane, nasararta shine samun salihan mutane wadanda za su koma ga Allah lafiya lau tsakaninsu da shi.
Amma da’awa zuwa ga komawa tsarin Allah din manufar Harkar ne, kamar yadda yake manufar dukkan Manzonnin Allah (T) ne.
Shaikh Zakzaky yana cewa: “Muna Da’awa ne (Mass Mobilization), mu muna ganin cewa su mutane a kan kansu ba su san ‘Power’ din da suke da shi ba, yanda yanzu misali Nijeriya da take da Musulmi fiye da miliyon 70, da sun san ‘Power’ din addininsu da su kansu, da za su yi magana da kalma daya, suce addininsu kawai zai yi iko da su, ba wani wanda ya isa ya dora musu wani abu ba addininsu ba. Ya kake gani?”
“Saboda haka hankoronmu shine mu wayar da kan mutane a kan wannan (su fahimci cewa suna da karfin da za su zabi abin da suke so ya yi iko da rayuwarsu).
Wato, idan mutane suka fahimci wannan kawai an samu sauyi.
Don yanzu da duk Musulmi za su fito su yi magana da murya daya suce Musulunci kawai muke so, ba wani wanda ya isa ya dora musu wani abu sabanin Musulunci din.”
Hanyar Cimma Hadafi:
To, akwai wasu abubuwa guda biyu, sune Principles da kuma Policy.
Shi Principles shine abubuwan da Harka Islamiyyah ta ginu a kansu, wanda sam ba za su taba canzuwa ba har abada, domin duk randa aka canza su, to an rushe Harka din. Muna iya cewa sune Hadafi.
Alal misali, Manufarmu itace tabbatar da addini a kan kanmu, da kuma ga al’umma baki-daya.
Wato muna so mu zama masu aikata addinin Musulunci a daidaikunmu da kuma burin samar da gwamnatin Musulunci. Kunga wannan Principle ne. A kan wannan ne da’awar ta ginu.
Don haka randa duk aka ce yanzu ba mu da burin yin addini a daidaikunmu, ko bamu da burin samar da gwamnatin Musulunci, to mun sauka ma hadafin. Mun rusa ‘principle’ dinmu kenan.
Amma shi Policy, shine hanyar da ake bi don kaiwa ga wannan hadafi ko cimma buri din. Misali, ta wace hanya za a mu bi wajen ganin mun tabbatar da addini din nan? Kila muce ta hanyar shirya wa’azozi, karatuttuka, Muzahara, raba takardu, da sauransu. Kun ga duk wadannan ‘Policies’ ne. Hanyoyi ne da muka zaba don mu kaima ga hadafi da burinmu.
To, idan muka canza Principle mun zanca Harka ne, amma idan abu ‘Policy’ ne, sai aka ga an yi shi a Harka Islamiyyah, to wannan bai kore Harkar ba, sai dai tana iya yiwuwa ya zama ‘Policy’ ne da ba zai kai mu ga cikar Principle din ko goal dinmu ba.
Misali, tana iya yiwuwa muce muna burin tabbatar da addini ne, wannan Principle ne mai kyau.
Amma kila sai mu ce za mu yi hakan ne ta hanyar shiga siyasa, mu rike mukamai, mu samu ‘yan majalisu da sanatoci da sauransu, sai mun yi karfi a cikin nizamin da ba ruwansa da Allah ba ruwansa da addini, sai kawai rana tsaka mu ce yanzu mun juya gwamnatin ta koma ta Musulunci.
Kun ga shiga siyasar a matsayin hanyar kaiwa ga manufa, Policy ne, amma Policy ne da ba zai taba kai mu ga ‘Goal’ ba.
Wani misali da Malam (H) ya bayar shine, kamar mutum ne yana Zariya, sai yace shi yanzu burinsa shine ya je Abuja (kunga Principle –burinsa- shine zuwa Abuja), amma sai ya kama hanyar Kano ya mike, kowa ya ganshi yace ina zuwa? Sai yace zan je Abuja! Kun ga bai canza manufa ba. Manufarsa ita ce zuwa Abuja, kuma ko mutuwa zai yi akan wannan manufar shi dai yana kanta, amma kuma ya kuskure ‘Policy’. Wato ya kuskure ma hanyar cimma manufar.
Da yawan wasu Da’awowin suna da Principle mai kyau, amma suna kuskure Policy ne, don haka saisu ruguje.
2- SHEKARU 40
Adadin 40 adadi ne mai muhimmanci a addinin Musulunci. Yana da wasu sirrika masu tarin yawa, wanda ba zan tsawaita bayani a kan su a yanzu ba, yana da kyau wasu Malamanmu su mana rubutu a kan muhimmancin 40 da sirrin da ke cikinsa.
Sai dai akalla, za mu iya fahimtar cewa akwai wasu boyayyun sirruka a cikin 40, a yayin da muka gano cewa:
A- An fara saukarwa da Manzon Allah (S) da wahayi ne bayan da ya cika shekaru 40 da haihuwa.
B- Tafiyar Annabi Musa (AS) shekaru 40 ne.
C- Annabi Musa (AS) ya tafi zuwa Duru Sina yai kwanaki 40.
D- An jefa Annabi Ibraheem (AS) a wuta ne na tsawon kwanaki 40, yayin da Allah ya umurce ta da ta zama sanyi da aminci a gare shi.
E- Annabi Dauda da Annabi Sulaiman kowannensu ya yi mulki ne na shekaru 40.
F- Imam Ali (AS) ya ruwaito daga Annabi (S) cewa; duk wanda ya haddace hadisai 40 da suka shafi al’amuran addini, kuma ya yi kokarin aikata su, Allah zai tashe shi a matsayin masani a ranar Alkiyama.
G- An ce mutum na zama cikakke ne mai kammalallen tunani a yayin da ya cika shekaru 40
H- Za mu ga akwai ruwayoyi masu yawa daga Ahlulbait (AS) da suke nuna duk wanda ya yi wani abu adadin kwana 40, ko kuma wanda ya yi wani abu, kamar hadisin Imam Bakir (AS) da yake cewa, wanda ya sha giya, Allah ba zai karbi sallarsa ba tsawon kwanaki 40.
I-To, akwai batun halwa na kwanaki 40 ma. Da cewa duk wanda ya nesanci aikata wani abu na tsawon kwana 40, ko kuma ya lizimci yin wani abu na tsawon kwana 40 a jere, wannan abin zai zama masa jiki.
Arba’in na da muhimmanci sosai, tana da sirruka masu yawa.
A takaice, wannan na defining terms din topic din da za mu tattauna ne a wannan zaure (Khairul Amal) a cigaba da bikinmu na murnar cikar Harka Islamiyyah shekaru 40 da Shelantawa.