Sama da mutane 100 ne suka rasu a jihohi biyu na kasar Indiya bayan sun sha wata nau’in Barasa. Jami’an tsaro da kafafen watsa labaran kasar sun tabbatar da aukuwar lamarin.
Rahotannni sun bayyana cewa mafi yawan wadanda suka rasu a Haridwar dake jihar Uttarkhand da yanki biyu dake da makwabtaka da Uttar Pradesh, sai da suka koka da matsalar ciwon ciki, daukewar numfashi da sauran cututtuka.
Ya zuwa yanzu jami’an tsaron sun kama mutane 4 da suke da alaka da mutuwar wadannan mutane a Haridwar kamar yadda wani babban jami’in dan Sanda mai suna Janmaijai Prabhakar ya shaidawa manema labarai.
A Haridwar kawai, an samu gawarwaki guda 36, a yayin da 18 suke ci gaba da karbar magani.
A hukumance ba a tabbatar da ko mutane nawa ne suka rasa rayukansu ba a yankin Uttar Pradesh, amma jaridun Indian Express da Times of India sun tabbatar da cewa; akalla mutane 69 ne suka rasa rayukansu a yankin Uttar Pradesh din.
An bayyana cewa; barasa wadanda ake siyarwa ba bisa ka’ida ba a kasar ta Indiya suna ci gaba da kawo asarar rayuka a kasar.
Rahotanni sun bayyana cewa; rabon da a samu irin wannan adadi na mutanen da suka rasu sakamakon shan barasa tun shekarar 2011 da a yammacin Bengal mutane 172 suka rasa rayukansu.