ABIN TAUSAYI;  Gobara ta kashe mutane 17 a wani Hotel

Gobara ta kashe mutane 17 a wani otel dake Indiya

daga Isa Musa

A kalla mutane 17 ne suka mutu a safiyar Talata sakamakon wata gobarar da tashi a wani otel dake unguwar Karol Bagh a Delhi dake Indiya.
Wadanda suka shaida lamarin sun ce a cikin wadanda suka mutu a gobarar akwai wata mata da yaronta wadanda suka yi kokarin tsalle ta taga.

Hukumomi a kasar sun bayyana cewa an ceto mutum 35, wasu sun samu raunuka wasu kuma an garzaya da su asibiti.
Wasu daga cikin bidiyon da wadanda suka shaida lamarin suka nada a wayoyinsu sun nuna yadda mutane ke tsalle daga ginin otel din.
Daya daga cikin jami’an kashe gobarar watau Vipin Kenta ya bayyana cewa a yanzu haka an fara gudanar da bincike a kan musabbabin gobarar.
Firai ministan kasar Narendra Modi ya bayyana jimaminsa a kan lamarin a shafinsa na Twitter.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *