Ambayyana Mahimmancin kafar yada labarai ga alumma
Daga Zubairu M.Lawal
Da yake jawabi ga alumman Duniya Sakatare Janaral na Majalisar Dinkin Duniya Mister Antonio Guterres ya yaba da irin rawara da kafafen yada labarai ta Radio ke badawa ga alumman Duniya.
Yace; hakika kowa ya kwana ya tashi da sanin gidajen Redio sunbada gudumawa mai yawan gaske a Duniya. Mister Antonio yace; dole ne mu tuna da wannan rana ta 13 ga watan Fabireru saboda shine ranar da aka kirkire kafar yada labarai ta bangare gidan Redio, wanda tabada gudumawa ga alumma wajen wayae da kain alumma,
Da kuma ilimantar da alumma da danar dasu abubuwa dayawa a duniya. Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yabawa kungiyar UNESCO saboda babban tunani na bunkasa yadda za’a wayar dakan alumma da suke ko ta ina a fadin duniya.
Ya kara da cewa sunyi amfani mai kyau wajen samar da hanyoyin isar da sako da alumma ke amfanuwa da ita a fadin Duniya.
Yace; a yau shirye-shiryen da kafafen Radio keyi yana ilimantar da alumma suna sanin halin da Duniya ke ciki kuma yana wayar dakan alumma ta fahintar wasu launukar al’dun wasu nahiyar da kuma nuna yadda ake zaman takewa da kowata irin kabila da nuna za,man tare.
Yace; tun a shekarar 1946 kafar yada labarai ta Redio a Duniya take taka mahimmiyar rawa wajen kawo cigaba a Duniya. Ya kara da cewa shirye shiryen gidajen Redio yana sauya tunani mutani daga mummunar abu zuwa kyakyawa.
Sakataren na Majalisar Dinkin Duniya yayi kira ga alumma dasu girmama wannan ranar ta 13 ga watan fabiraru akuma yawaita yin adu’o’I da nuna cigaban.