SIYASA RIGAR YANCHI;  Zamuyi aiki da kowata kabila domin cigaban Nasarawa

Zamuyi aiki da kowata kabila domin cigaban Nasarawa

Daga  Zubairu M. Lawal

Tsohon Ministan yada Labarai  kuma xan takarar Gwamnan jihar Nasarawa Honorabul Labaran Maku na jam’iyyar APGA.

Yace; idan Allah yabashi sa’a ya kafa Gwamnatina a jihar Nasarawa zai hada kowa da kowa a tafi tare a cikin Gwamnati saboda kowata kabila kabata hakinta na zama xan jihar domin cin gajiyar mulkin demukurdiyya.

Maku yace; Allah yayimu tare kuma yan jihar daya masu manufa daya baiga dalilin da zamu riqa rikici da juna ba.

Kamata yayi mu hada kai saboda babu abinda yake kawo cigaba a jihar kamar hadin kai.

Labaran Maku yace; meyasa a lokacinda muke hade da jihar Pilato muke zaman lafiya kuma muke kaunar juna? Amma yanzu muna da jihar tamu ta kanmu amma ya zama matsala sai fada da zub da jini .

Labaran Maku ya kara da cewa yana tausayin yankin Arewacin Nijeriya. Saboda rigingimu sunyi yawa kullun yan Arewa na kashe yan Arewa.

Tun daga  jihar Benuwe zuwa jihar Barno daga jihar Nasarawa zuwa jihar Sokoto kullun kisa akiye meya same Arewa ne ?

Haka magabata irinsu Sardauna da Tafawa Balewa suka koyar damu ? Ya kamata yan Arewa manya da yara muyi nazari .yanzu yankin Kudancin Nijeriya sunyi mana nesa. Suna da ilumi ga zaman lafiya .

Amma yankin Arewa yaranmu basu zuwa makaranta babu ilumin mune cibaya a vangaren ilumi haka zaliqa mune  cibaya a vangaren zaman lafiya .

Labaran Maku ya umarci dubban alumman da suka halarci gangamin yakin niman zavensa a yankin Nasarawan Eggon da su fito kwai da kwarkwata a ranakun zave saboda su zave yan takara na gari wadanda suke jam’iyyar APGA.

Ya kara da cewa 2019 za’ayi a kasa a tsare a raka kuma a tabbatar sai an sanar sannan jama’a su bar wajen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *