Yan Bindiga sunyi garkuwa da wasu motochi dauke da kayan zabe
Daga Ibrahim Lawal
Labarin damuka samu a yanzu na cewa a yau din nan wasu yan bindiga sun kai mumunan hari kan wata motar hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta wato INEC, a jihar Benuwe, yayinda ake raba kayayyakin zabe kananan hukumomi. Kwamishanan hukumar INEC na jihar,
Dr. Nentawe Yilwatda, ya bayyana hakan ne yayinda yake magana da manema labarai a jihar. Yace motar na dauke da kayayyakin zabe irinsu alkaluman rubutu, kayayyakin jami’an zabe, huluna, akwatinan zabe da sauransu.
“Wannan gaskiya ne, an kaiwa motarmu hari yayinda ake safarar kayayyakin aiki a unguwar Logo kuma wasu mutane ne sanye da kayan sojoji.”
Kumji cewa a yaune Yan sanda suka kama wata mota dauke da katin zabe da aka dangwa a jihar kano.