Fadar shugaban kasa da APC na shirin tsige shugaban hukumar INEC -Yakubu Dogara
Daga Aliyu Mustapha
Hon. Yakubu Dogara ya zargi fadar shugaban kasa da jam’iyyar APC, na kulla makircin kunyata INEC, ta hanyar tunbuke Farfesa Mahmood Yakubu daga ofishinsa
– Ya kuma yi tsokaci kan furucin Buhari na cewar duk masu kudurin satar akwatunan zabe su shirya yin hakan a bakin rayuwarsu
– Dogara ya kuma ce sun gano cewa fadar shugaban kasa da APC na matsin lamba ga INEC akan ta gudanar da zabe a wasu jihohi ta kyale wasu
Kakakin majalisar wakilan tarayya, Hon. Yakubu Dogara ya zargi fadar shugaban kasa da jam’iyyar APC, na kulla makircin kunyata hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta hanyar yunkurin tunbuke shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu daga ofishinsa.
Ya kuma bayyana wani furuci da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a wani taron kusoshin jam’iyyar APC, a ranar Litinin, na cewar duk masu kudurin satar akwatunan zabe su shirya yin hakan a bakin rayuwarsu, a matsayin daukar mataki da hannu, yana mai cewa kalaman shugaban kasar sun sabawa kyakkyawar demokaradiya ta kasar.
Da ya ke jawabi a wani taron manema labarai a ofishin yakin zaben dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP, a Maitama, Abuja, Hon. Dogara ya yi Allah-wadai da zargin da shugaban kasa Buhari da shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole su ka yi na cewar PDP na da masaniyar matakin INEC na dage zabe tun kafin ranar.