Batun satan akwatin zave Gwamnan Benuwe ya gargadi jami’an tsaro kada su taba yan jiharshi.

Batun satan akwatin zave Gwamnan Benuwe ya gargadi jami’an tsaro kada su taba yan jiharshi.

Daga Madina Ibrahim

Gwamna Samuel Ortom ya gargadi jami’an tsaro da su bijirewa umurnin shugaban kasa Buhari na kashe barawin akwatin zave

Ortom ya ce idan har jami’an tsaron suka bi umurnin shugaban kasar to hakan zai janyo hukunci mai matsanani daga kotun ICC

Ya jaddada cewa a shirye su ke domin zubar da jininsu na karshe ma damar zai haifar da dorewar demokaradiyar kasar

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya gargadi jami’an hukumar tsaro ta fararen kaya (DSS), Rundunar ‘yan sanda da rundunar soji da dama sauran jami’an tsaro da su yiwa kawunansu karatun ta-nutsu tare da bijirewa umurnin Buhari na kashe duk wani barawon akwatin zave a yayin gudanar da zabukan kasar mai zuwa.

Ortom ya ce jami’an tsaro su bi umurnin shugaban kasa Buhari na daukar mummunan mataki akan barayin akwatunan zave zai kara yawan adadin kisan ‘yan Nigeria ba bisa ka’ida ba, yana mai cewa hakan zai janyo hukunci mai matsanani daga kotun hukunta masu aikata laifukan ta’addanci ta qasa-da-qasa (ICC).

Da ya ke jawabi ga manema labarai a ranar Talata a Abuja, gwamnan ya ce ya zama wajibi rundunar soji da sauran jami’an tsaro su bi dokokin da ke zagaye da zabukan, yana mai cewa ba ya goyon bayan satar akwatunan zave amma bin matakan da doka ta tanadar shi ya fi mai mamakon daukar mataki a hannu.

“Ina sane da cewa APC na shirin baiwa sojoji da sauran jami’an tsaro kariya domin goyon ban ‘yan APC da gallazawa jam’iyyun hamayya. Ba zamu amince da hakan ba.

“Ya kamata ‘yan Nigeria su sani cewa da yawan su a shirye su ke domin zubar da jininsu na karshe ma damar zai haifar da dorewar demokaradiyar kasar.

“Gwamnatin da aka zave ta karkashin demokaradiyya na shirin sauyawa zuwa salon mulkin mallaka. Abun takaici ne ace shugaban kasarmu shi ne zai fito yana furucin da suka sabawa dokokin kasa da kuma kara haddasa kashe kashen rayukan ‘yan Nigeria da haddasa kazamin rikici a tsakaninsu,” cewar Ortom.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *