Ana ta harbin bindiga yayinda magoya bayan APC da PDP suka kara a Nasarawa
Daga Aliyu Mustapha
Magoya bayan jam’iyyu biyu masu karfi All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) sun kara da juna a jihar Nasarawa
Anyi harbe-harben bindiga da dama wanda yayi sanadiyar lalata ababen hawa da kuma tarwatsewar alumma kowa yayi ta kansa .
Rikicin ya kaure ne lokacin da magoya bayan jam’iyyun biyu ke gudanar da gangamin yakin niman zabe a garin.
yayinda ake shirin rufe kamfen din yan takarar gwamna da na majalisar dokokin jiha a gobe alhamis .
Aran gamar ya farune a Karamar hukumar Obi dake jihar Nasarawa a yau laraba.
Koda dai babu wanda aka raunata ko aka kshe yayin rikichin , majiyarmu ta lura cewa harbin bindigan anyitayine a sararin samaniyya sai dai yakan fado kan ababen hawa .