SAKON Kwamishinan Yan Sanda A sanar da sakamakon zaben Kano kafin Sallar Isha’i
Daga Zubairu M Lawal
Kwamishinan yan sandan jihar Kano, Mohammed Wakili ya bayar da umurnin cewa a sanar da sakamakon zaben jihar Kano kafin Sallar Isha’i.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar kalubale wajen bayyana sakamakon zaben gwamna a jihar
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano wanda ake yiwa inkiya da maza kwaya, mata kwaya, Mohammed Wakili ya bayar da umurnin cewa a sanar da sakamakon zaben jihar Kano kafin Sallar Isha’i kamar yadda shafin BBC Hausa ta ruwaito.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun kalubale dangane da bayyana sakamakon zaben jihar.