Zanyi aiki da kowa a jihar Nasarawa – A.A. Sule

Zanyi aiki da kowa a jihar Nasarawa – A.A. Sule

Daga Zubairu M Lawal

Bayan kammala fadin sakamakon zaben ne Zabeben Gwamna mai jiran rantsarwa Injiniya Abdullahi Sule yayi ganawar gaggawa da manema labarai a ranar Littinin , inda ya nuna godiyarsa ga alumman jihar Nasarawa da suka zabe shi.
Abdullahi Sule yace; ya tabbata alumman Jihar Nasarawa sun nuna masa kauna . Saboda sun fito sun zabe shi ba tare da yin la’aqari da vamvamcin addini ko qabilaba.

Yace; zai gudanar da harkokin Gwamnatinsa da kowa da kowa. Ya qara da cewa ; kamar yadda yake fadi zai lokacin yakin niman zabe cewa ; zai farfado da harkokin haqar ma’adanai saboda ta nanne jihar zata samu kudaden shiga mai yawa.

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta tabbatar da nasarar Alhaji Abdullahi Sule na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan jihar Nasarawa wanda ya gudana a ranar Asabar da tagabata.

Baturen zabe Farfesa Abdullahi Bala ya tabbatar da nasarar Injiniya Abdullahi Sule wanda ya kada abokan karawarsa na Jam’iyyar PDP Devoid Ombugadu da Labaran Maku na jam’iyyar APGA.

Baturen zaben wanda shine Shugabn jami’ar Gwamnatin tarayyar dake Minna jihar Niger, yace Dan takarar Gwamna a jam’iyyar APC Wanda yayi nasarar ya samu kuri’a 327,229

Yayin da Mister Devid Ombugadu na jam’iyyar PDP yazo na biyu da kuri’a 184,281

Hon. Labaran Maku na jam’iyyar APGA yazo na uku da kuri’a..132,984

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *