Alhakin fadin sakamakon zabe na wuyan INEC ne – Sarkin Kano
Daga Aliyu Mustapha
Biyo bayan rashin tabbatar da sakamakon zabe, Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi,ya yi kira ga daukacin al’ummar jihar Kano da su kwantar da hankali tareda zama cikin nutsuwa domin baiwa hukumar zabe damar gudanar da aikinta.
Yayin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta kaddamar dacewa zaben wasu jihohin kasar nan bai kammalaba, Sarki Kano yayi kira ga daukacin al’ummar Najeriya da su kwantar da hankullansu wajen baiwa hukumar INEC damar sauke nauyin da ya rataya awuyanta.
Cikin wata hira afarfajiyar fadar sa yayin ganawa da manema labarai, MaiMartaba Sununi yace hukumar INEC kadai ke da alhakin hukumance na sauke nauyin gudanar da zabe tare da bayyana sakamakonsa. Yayi kira da abai wa INEC damar gudanar da aikin ta.
A jiya Litinin hukumar INEC ta kaddamar da cewa zaben gwamnan jihar Kano da aka gudanar aranar Asabar data gabata bai kammala ba sakamakon yadda adadin kuri’u da aka soke yahaura adadin kuri’una tazara da ketsakanin manyan’ yan takarar biyu masu rin jayen samun nasara.
Cikin zayyana dalilai na soke wasukuri’u, Farfesa Riskuwa Shehu wanda ya kasance Baturen zabe na jihar kuma shugaban Jami’ar jihar Kebbi yace,hakan ya bayune sakamakon hargitsi da kuma maimaicin kada kuri’u da suka auku awasu mazabu cikin kananan hukumomi 22 dake jihar Kano.
Sarki Sunusi ya yabawa kwazon Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Muhammad Wakil da kuam sauran hukumomin tsaron dan ganeda muhimmiyar rawar gani da suka taka wajen tsarerayuka gami databbatar da zaman lafiyar al’umma alokuta na zabe.