APGA ta qalubalanci Sakamakon zaven Nasarawa

APGA ta qalubalanci Sakamakon zaven Nasarawa

Daga Abdullahi Baba

Xan takarar kujerar Gwamnan jihar Nasarawa a jam’iyyar APGA wanda yazo na uku da kuri’a 132,984 a zaven da ya gudana a ranar Asabar da tagabata, ya fito ya qalubalanci wanan sakamakon da cewa harantaciyar sakamakon ne.
Honorabul Labaran Maku yace; sakamakon zaven abune wanda hankali ba zai dauka ba.

Labaran Maku yace ; wanan sakamakon zama akayi aka rubutashi ba sahihin sakamakon da aka gudanar da zaven bane. Ya kara da cewa siyasa tsarine da akaba mutani damar su zave wanda sukeso ya mulkesu a kowani matsayi.

Labaran Maku yace; muke da alumma vangaren Gwamnati bata da alumma saboda batayiwa alumma komai ba.
Alumman karkara suna fama da wahala babu abinda Gwamnati tayi masu babu hanya babu wuta babu ruwa Gwamnati bata zaiyartarsu bare tasan matsalarsu.

Yace; mun zagaya lungu sako Jama’a sun bayyana mana damuwarsu Kuma sun zave mu . Basu zave APC ba saboda ta takurawa rayuwarsu . Ta hanasu albashi tana masu biyan wulaqanci, ta hana tsofafin ma’aikata haqoqinsu.
Labaran Maku yace; muna da hujoji, da suka tabbatar da cewa wanan sakamakon na Bogene , gaskiyar magana. Yace ; bazamu amince da wanan sakamakon ba zamu garzaya zuwa kotu saboda mu karbi haqinmu.

Da aka tambayeshi cewa ; suna da gamsasun hujjoji da zasu gabatar a kotu ?

Labaran Maku yace; muke da hujja shiyasa kaga har muke magana, sauran jam’iyyar da basu da hujja kuma basuje ko’ina ba a zaven sai dai aka rubuta aka basu ai basuyi magana ba.
A 2015 ance bamu da hujja komunje kotu bazamuyi nasara ba amma mukaje kotu ,kuma shedar Al-makura suma a kotun suka tabbatar da magudin da APC tayi.

Duk da cewa; kotun batayi mana adalciba a wanan lokacin kuma muka barwa Allah to yanzu ma zamuje kotun kuma muna fatan kotu zatayi mana adalci.

Daga karshe Maku yace ba zamu kyele a walaqanta harkokin Demukurdiyya a jihar Nasarawa ba zamu cigaba da fafutukar siyasa har sai mun kwatowa alumman jihar Nasarawa yanchi .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *