SAKAMAKON ZABE -INEC ta bayyana PDP a matsayin ta lashe zaben Jihar Imo

SAKAMAKON ZABE -INEC ta bayyana PDP a matsayin ta lashe zaben Jihar Imo

Daga Aliyu Mustapha

Tsohon kakakin majalisar wakilan Najeriya,Emeka Ihedioha na jam’yyar PDP ya samu nasarar lashe zaben Gwamnan jahar Imo daya gudana a ranar Asabar, 9ga watan Maris, kamar yadda Baturen zaben FarfesaFrancis Otonta ya bayyana.

Duniyarmuayau ta ruwaito Farfesa Otonta ya bayyana haka ne da sanyin safiyar Talata a cibiyar tattara alkalumman sakamakon zaben Gwamnan jahar dake garin Owerri, babbanbirnin jahar Imo.

Dayake sanar da sakamakon zaben, Otonta yace Emeka Ihedioha na jam’iyyar PDP ya lashe zabe akananan hukumomi goma shadaya cikin ashirin da bakwai na jahar Imo, inda yasamu jimillar kuri’u 273,404.

Wanda ya zo na biyu awannan zabe kuwa shine surukin Gwamnan jahar Imo,Rochas Okorocha,Uche Nwosuna jam’iyyarAA,wanda ya lashe kananan hukumomi goma, tare da samun kuri’u190,364, yayin da tsohon Gwamnan jahar Ikedi Ohakim na jam’iyyar Accord ya tashi da kuri’u 6, 846 kacal!

Dan takarar jam’iyyar APC, Sanata Hope Uzodinma kuwa shi yazo na hudu da kuri’u96,458,yayin da na ukun su shine Ifeanyi Ararume daga jam’iyyar APGA, wanda yaci kananan hukumomi guda hudu tare da samun kuri’u 114,676.

A gabadaya zaben an kada kuri’u739,474, inda daga ciki aka samu haram tattun kuri’u 25,130,sai kuma sahihai guda 714,344, kamar yadda Baturen zaben FarfesaFrancis Otonta ya bayyana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *