Majalisar xinkin Duniya ta yabawa alumman Nijeriya yadda akayi zabe lafiya
Daga Zubair M Lawal
Majalisar Dinkin Duniya ta yabawa alumman Nijeriya yadda suka gudanar da zabe lafiya ba tare da hayaniya ko tashin hankali ba.
Mister Muhammad bin Chambas shi ya wakilci Majalisar xinkin Duniya yayi gudanar da zabe a tarayyar Nijeriya.
Yace; alumman Nijeriya sun nunawa Duniya cewa alumma ne masu bukatar zaman lafiya da juna. Yace; sun gudanar da zabuka batare da tada hankali da zai kai ga zubda jini ba.
Ya kara da cewa; Majalisar Dinkin Duniya ta ji dadin yadda alumman Nijeriya suka gudanar da zabe cikin nutsuwa.
Yace; kafin zabe kungiyoyi da dama sunyi ta kiraye-kiyare na zaman lafiya a birni da karkara. Yace; alumma sun ansa kiran da kungiyoyin kuma sun gudanar da zaben lafiya .
Yace; babu zaben da akafi jin tsoron abinda zai biyo baya kamqr zaben Shugaban qasa da ya gudana .
Yace; an samu hadinkai da cigaba a Nijeriya saboda yadda alumma suka hada kai suka gudanar da zabe lafiya batare da zubar da jini ba. Yace; wanan ya nuna yadda Demukurdiyya ya samu karbuwa gurin alumman Nijeriya.
Yace ; Majalisar Dinkin Duniya ta taya alumman Nijeriya murna ta kuma yabawa dukkan yan takarar saboda yadda suka rungumi akidar zaman lafiya .
Muhammad Chambas yace ; suma jam’iyyun da basuyi nasara ba sun kwantar da hankalinsu, basu dauki mummunar mataki ba . hakama masu fada aji sun taka rawa wajen janyo hankalin alumma domin zaman lafiya .
Yace; siyasa akwai nasara akwai rashin nasara , dole alumma su fahinci haka. Kuma duk wanda bayyi nasara ba yadauki matakin hakuri, dabin ka’idoji idan da matsala .
Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin dake yankin Afirka sun tabbatar da samun zaman lafiya a zabukar . Hakama kungiyoyin sanya Ido da sauran su sun nuna yadda alumma sukayi zabe cikin nutsuwa .