DAGA KOTU YAZAMA –  sabon Sarkin Lafian Barebari

Daga Kotu ya zama    sabon Sarkin Lafian Barebari

Daga Zubairu M. Lawal

Mai shari’a Sidi Bage ya zama sabon Sarkin mai daraja ta daya a masarautan Lafian Barebari dake jihar Nasarawa.

Tum bayan rasuwar Sarki Isa Mustapha Agwai na daya ake ta tunanin wanda zai gaji wanan kujera mai tarihi a jihar Nasarawa.

Marigayi Alhaji Isa Mustapha Agwai ya rasu cikin watan Janairu ranar 10/1/2019  bayan duguwar rashin lafiya da yayi fama dashi. Ya kasance wanda yafi kowa dadewa kan karagar mulkin yana da shekaru 44 akan mulkin.

Tsohon Sarkin ya rasu yabar yara biyu Mace da na miji.

Tun bayan rasuwarsa ake tunanin wanda zai gaji kujerar.

Alhaji Sidi Bage ya zama Sarki na 17 a masarautan Lafiyan Barebari, wanda aka nadashi  ayau Talata, bayan zaben Sarki da masu zaben suka gudanar.

Alhaji Sidi Bage kafin ya zama Sarki yayi aiki aBabban  ma’aikatan Shari’a ta kasa ( Supreme Court judge).

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *