KU KARANTA YADDA – Gobara tayi barna a sansanin yan gudun hijira

Gobara tayi barna a sansanin yan gudun hijira

Daga Zubairu T.M.Lawal Lafia

A kwanaki bayane mumunar gobara ta afku a sansanin yan gudun hijira dake garin Mangunu a jihar Barno. Gubarar ta farune sanadiyyar wutan girka abinci da wasu mazauna sansanin suke gudanara da girka abinda zasukai bakin salati.

Gubarar ta farunea kusa da inda ake ajiyan kayayakin amfani nay an gudun hiji da ma’aikatan Agaji na Majalisar [inkin Duniya ke amfani dashi domin bada agaji garesu.

Gubarar ta fantsamane zuwa gurare da dama day a hada da dakunan yan gudun hijirar da kuma wuraren ajiyar kayan agajin dama filin wasansu.

Gubarar ta janyo asarar rayukan mutum uku kanana biyu da Babba daya da kuma kayan abinchi da kayan kwanciya. Kimanin mutum 900 ne suka hadu da asara a wanan mummunar gobarar.

Sansanin dai yana fama da cinkoson yan gudun hijira kimanin mutum 8000 wanda hakan kan janyo masu cikas wajen gudanar da wasu abubuwa nay au da kullun.

Sakataren Majalisar [inkin Duniya Mistar Antonio Guterres, ya nuna alheni da tausayawa  akan dubban mutanin da gobarar ya rutsa dasu a sansanin yan gudun hijirar. Da yake Magana a ta bakin mai kula da bangaren hakin [an Adam a Nijiriya Mistar Edward Kallon   yace; wanan gobarar da ta afku ta kara maida hannun agogo baya saboda yanzu komai zai tsaya cif.

Ya kara da cewa ; wajibine a samar da wani matsu guni na masamman ga ilahirin yan gudun hijirar da yanzu suke cikin wanan sansanin day a kone kuma dubban alumma sune zama a cikin kunci saboda rashin gurin kwana.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *