Sarkin Obi ya yabawa aikin tawagar Likitan Talakawa
Daga Zubairu M.lawal
A ranar Juma’a ne tawagar Likitotin dake aikin kiwon lafiya kyauta suka ziyarci Sarkin Obi Alhaji Aliyu [an Giwa Ogiri Orume. Tawagar dai ta kasance a garin na Obi dake a jihar Nasarawa tun a ranar alhamis ne }ar}ashin Dokton Talakawa Honorabul Joseph Haruna Kigbu tsohon [an majalisar day a wakilci mazabar Lafia da Obi.
Tawagar ta isa fadar Sarkin ne da misalign karfe 9;30am. Jagoran tafiyar Honorabul Joseph haruna Kigbu ya mi}e yayiwa Sarkin godiya da samun lokacin da yabasu kuma ya fito. Yace; mun iso garin Obi ne tun a ranar alhamis danufin tallafawa alumman wanan yankin baki daya, ta bangaren kiwon lafiya.
Ya }ara da cewa a jiya kawai mun samu nasarar duba mutani kimanin dari biyar, cikin tawagar akawi Likitochi dabam dabam da suke aiki a fannoni na kiwon lafiya kuma kwararu.
Dokto Joseph Haruna Kigbu yace; “bisa alkawarin da na daukawa alumman garin Obi da kewaye a lokacin yakin niman zabe nace idan suka zabeni insha Allah bayan zabe zan zonan garin na gudanar da harkan kiwon lafiya kamar yadda muke gudanarwa a wasu jihohi”
“Ya kara da cewa gashi Allah ya bamu ikon zuwa mu cika maku al }awarin da muka dauka maku”.
Shima a nasa jawabin Sarkin garin Obi Alhaji Aliyu [an Giwa Ogiri Orume, yace; ya godewa wanan tawaga mai albarka kuma yana rokon Allah ya }arama wanan tanagar albarka da }warin giwa na ayyukan alfarma da takeyi a fadin }asan nan.
Ya }ara da cewa babban abin farin cikine ga alumman jihar Nasarawa cewa ayau gashi [an jihar ne yake jagorantar wanan tawaga ta Likitochi mai suna ( Doctor on the Mover Africa), kuma yana gudanar da ayyuka yadda ya dace a fadin }asanan .
Sarkin ya kara da cewa a girare dabam dabam ana maganar wanan tawagar saboda ayyukan alheri da takeyi. Yace; muma yau muna alfahari da wanan tawagar kiwon lafiya da tasauko wanan gari. Kuma muna godiya da manya manyan likitochin da suka ziyarce mu.
Alhaji Aliyu [an giwa Orume ya }ara da cewa munyi murna da kacika wanan alkawarin da ka daukawa alumman garin Obi , yace; haki}a alumman Obi sun }aunace ka saboda sun yaba da ayyukan ka a zaben da akayi na 2011 da ka tafi majalisa jama’a sun amfana da mulkika sosai.
Shiyasa banama da kazoo nima wajen jama’a baka samu tangarda ba saboda jama’a suna duba mutumin day a damu da damuwarsu su kuma amince day a wakilcesu. Kuma muna rokonka cewa shari’a da akeyi idan Allah ya baka to ka cigaba da ayyukan alheri da kakeyi.
Kuma ka rungume alumman mazabarka kowa ya zama naka, idan kuma ba’a samu nasara a wajen shari’a ba to ka zama mai hakuri saboda gaba tana dayawa. Duk abinda kaga ka samu dama Allah ya rubuta zaka sameshi idan kuma ka rasa to Allah ya rubuta zaka rasashi, idan kayi hakuri sai ya musanya maka da wani babba mafi alheri.
[an haka muke rokonka ayyukan alheri da kakeyi kaci gaba da yinsa Allah ne kadai zai biya ka kuma zai baka abu mafi alherin wandama kake nima.
Tawagar likitan talakawa tayiwa samada mutum 1200 Tiyata a Ido kyauta, hakama wadanda idanunsu ba sai anyi aiki bad a wadanda aka basu madubin kallo na ido. sanan sama da mutum 100 manyan da yara akayiwa aikin Tiyata. Daruruwan jama’a ne suka samu magunguna a wanan ayyukan da tawagar (Doctor on the Mover Africa ) ta gudanar.