Kalaman Sheakh Zakzaky na batun Zamfara ya mamaye  Social Media

Kalaman Sheakh Zakzaky na batun Zamfara ya mamaye  Social Media

Daga Ibrahim Lawal

ALAKAR ZAMFARA DA MALAM ZAKZAKY.

Nayi fira da wani babban farfesa a bangaren kimiyyar siyasa na jami’ar bayero ta kano kuma ya bankade min wasu muhimman batutuwa da ya kamata al’umma ta sani.

•Na farko yace lallai da bukatar al’umma ta gano alakar doguwar tsarewar da ake ma jagoran ‘yan shi’a ibraheem zakzaky.

•Da alamun shakku gami da taraddudi bisa takamaiman alakar case din malam zakzaky da rikicin zamfara.

•Shekaru shidda da suka wuce malam zakzaky yayi hasashen faruwar abubuwan dake faruwa a zamfara kuma gashi yanzu kwabo da kwabo suna faruwa.

•A hasashen da malamin yayi ya nuna ba a zamfara kurum aka shirya makamancin wannan shiri ba.

•Kuma tun wancan lokaci da malamin yayi wannan hasashe ansha jiyo shi yana balokokon ana neman rayuwar sa.

•Shekara uku da hakan incidence din zariya na 2015 ya faru, tun lokacin sau daya aka kuma jin duriyar sa.

•Yanzu gashi ana ta kashe kashe a zamfara kamar yadda ya fada.

•Saboda haka idan ba an nemi sanin hakikanin lamarin daga wajen sa ba zuwa gaba lamarin yana iya kazanta fiye da hakan.

•Saboda haka yace a sanar da masu zanga zangar a saki malam zakzaky da masu zanga zangar zamfara su hade waje guda tukuna su nemi a basu dama sheikh zakzaky ya fito yayi fashin baki da karin bayani bisa wannan yanayi.

•Farfesan yace wannan aiki ne daya hau kan almajiran malam zakzaky da kuma mutanen zamfara saboda zuwa yanzu sune abin yafi shafa kai tsaye.

•Ya kara da cewa dole ne mutanen zamfara su hada kai da almajiran malam zakzaky kowanne daga cikin su ya zama dan mediya na karfi da yaji domin aikin wayar da kan al’umma bisa wannan lamari ya rataya ne a wuyan su.

*_A karshe babban farfesan yayi gargadin cewa: idan har ba’a takura gwamnati ta fito da malam zakzaky ya fadi mafitar wannan lamari to da yiyuwar abin ya kazanta matuka kuma ba zai tsaya iya zamfara ba zai mamaye arewa ne gabadaya!!!_*

WANNAN BA MAGANAR AKIDAR ADDINI BACE MAGANAR CETO AREWA NE!!!

DON ALLAH A YADA WANNAN SAKO.

 

Go to Home
Rariya
MALLAMI WALIYIN ALLAH.
Shekaru 6 Da Suka Gabata Shaikh Zakzaky Ya Tabbatar Mana Da Cewa “Zamfara Akwai Zinare Akarkashin Kasa Da Sauran Ma’adinai”.
~ Daga Aminu Idris Yunusa
“Yace Amurka na so ta zo ta saci dukiyar wajen don haka za ta yi amfani da ta’addanci ne sai daga baya su zo da sunan sun zo magance ta’addanci su yi sansani bayan sun tada garuruwan mutane, su rika diban ma’adanai suna fita da suwaje…
Don me kuke kashe bayin Allah don kawai ku saci arzikin da ke karkashin su?
Tabbas tsare Shaikh Zakzaky na da alaka sosai da kashe bayin Allah da ake a Zamfara…
Saboda inyana waje sam ba zai yi shiru ba, duk motsin da Hukuma ko iyayen gijinta (Amurka da Isra’ila) suka yi na sata ko ta’addanci sai ya bayyanawa al’umma matukar yasani…
Allah kasa mudace…
Yesterday at 7:03.

Zamfara
Ina laifin ku zo ku haƙi arziki ku sata ku fita da shi, amma ku bar mutane da ransu? Don me sai kun tashe su daga garuruwansu ta hanyar kisa da kona gari?
Shekaru 6 da suka gabata Shaikh Zakzaky ya tabbatar mana da cewa Zamfara akwai Zinare a karkashin kasa da sauran Ma’adinai.
Yace Amurka na so ta zo ta saci dukiyar wajen. Don haka za ta yi amfani da ta’addanci ne sai daga baya su zo da sunan sun zo magance ta’addanci su yi sansani bayan sun tada garuruwan mutane, su rika diban ma’adanai suna fita da su.
To ku zo ku sata mana kawai ku kyale mutane da ransu? Don me kuke kashe bayin Allah don kawai ku saci arzikin da ke karkashin su?
Tabbas tsare Shaikh Zakzaky na da alaka sosai da kashe bayin Allah da ake a Zamfara. Saboda in da yana waje ne sam ba zai yi shiru ba, duk motsin da Hukuma ko iyayen gijinta (Amurka da Isra’ila) suka yi na sata ko ta’addanci sai ya bayyanawa al’umma matukar ya gano.

Ya kamata dai masu fada aji da mahukunta dama talakawa ayi nazari kan wanan maganar

Idan ana buqatar mafita na gaskiya sai  a je gareshi a nema domin masu iya magana sunce durkusama wada ba gajiyawa bane .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *