Ni Ba Yar Madugo Bace ___ Jaruma Hadiza Gabon
Daga Ibrahim Lawal
Jarumar da tauraruwarta ke hasakawa Hadiza Gabon tace ita Ba Yar Madugo Bace, Bata Shaye Shaye Bata Karuwanci Kuma Bata Neman Mata. Ita Mutuniyar Kirkice.
Jarumar tayi wannan furucin ne bayan rikicin daya barke a Hausa Film industry. Kalaman ya biyo bayan hoton da Jaruma Amina Amal ne tasa a shafinta na Instagram inda ta bayyana tsiraicinta. Inda ita Hadiza da wasu yan film suka yi ca a kanta. Inda suke nuna mata hakan bai dace ba.
A cikin martanin da Amal din ta bayar har take nuna ai gara ita da wasu matan da suke neman mata yan uwansu a Kannywood din.
Inda wannan kalaman ya fusata Hadiza Gabon din har tasa aka kamota ta wanwanka mata mari.
Duk da kasancewar Amal din bata kira suna ba amman ita hadizan tace da ita ake wannan zancen, wanan ya sanya itama ta wallafa nata kalaman a zuwan kare kai.
Rigingimu dai na cigaba da kunnokai a Kannywood . ba mazan ba ba matanba .