KO KUNSAN – An samu kyaukyawar fahintar juna : tsakanin Ali Nuhu da

KO KUNSAN – An samu kyaukyawar fahintar juna : tsakanin Ali Nuhu da Adam Zango

Daga Madina Ibrahim

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa an yi sulhu a tsakanin manyan jaruman nan na masana’antar shirya fina-finan Hausa, wato Ali Nuhu da Adam A. Zango a garin Kano, bayan gumurzun da suka tafka.

Hadakar kungiyar nan ta masu shirya fina-finan Hausa ta kasa wacce aka fi sani da MOPPAN karkashin jagorancin Abdullahi Maikano ce ta yi nasarar shirya jaruman biyu.

Anyi hakan ne a ofishin jigon Kannywood kuma shugaban majalisar amintattu na kungiyar, wato Malam Abdulkarim Mohammed a yau Asabar, 13 ga watan Afrilu.

Sakataren kungiyar MOPPAN reshen jihar Kano, Malam Salisu Officer, ya tabbatar da hakan ga manema labarai, ya na mai cewa, yanzu Ali zai janye karar da ya kai Adamu a kotu.
A baya kunji cewa, Ali Nuhu ya yi karar Adam A Zango a kotu kan cewa kotu ta shiga tsakaninsa da Zango kuma ya daina ba ta masa suna.

Wannan na dauke ne cikin takardan kirar kara wanda Ali Nuhu ya shigar a kotun USC da ke Fagge a Kano.

Kotun ta bukaci Adam Zango ya gurfana gaban a ranar 15 ga watan Maris na 2019 misalin karfe 8.30.

Yanzu dai Ali Nuhu zai iya janye karar da ya shigar tunda an samu maslaha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *