Jami’an tsaro a Jihar Kaduna sun kama Yara Almajiran Shaikh Zakzaky sama da 40 jiya Lahadi*

*Jami’an tsaro a Jihar Kaduna sun kama Yara Almajiran Shaikh Zakzaky sama da 40 jiya Lahadi*

Daga Wakilinmu

Da yammacin jiya Lahadi yara kanana Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) wadanda ake kiransu da yan Intizar suka fita domin gudanar Murnar su na Samuwar Imamin Karshe cikin Jerin Imaman Shiriya Sahibul Asr, tare da nuna farin ciki da samuwar Jagoran Harkar Musulunci Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), inda suka nufi guri na musamman domin wannan Bikin kamar yanda suka tsara zasu gudanar.

Sai dai bayan kammala taron nasu da suka tsara Jami’an tsaron yan sanda sun kama su a dai-dai ‘Constitution road’ dake Kabala West a cikin garin na Kaduna, inda suka tsare su tun jiya ba’a san inda suke ba sai yau aka gano inda suke kana kuma daga baya suka dauke su zuwa ‘State CID dake nan cikin garin na Kaduna.

Wadannan yara da Jami’an tsaro suka kama dukkan su masu karanan shekarune ciki kuwa harda masu shekaru biyar zuwa bakwai, wadanda adadinsu ya kai kimanin 43. Zuwa hada wannan rahoton dai babu wani kwakkwaran Hujja da Jami’an tsaron suka bayar sai dai Hujjar kawai an Haramta Shi’a a Jihar ta Kaduna.

Muna barar addu’oin yan Uwa na Allah ya kubutar da wadannan yara da gaggawa. A lokacin da Jihar Kaduna ta rikice da sace mutane da Garkuwa dasu ita kuma Gwamnatin damuwarta kama kananan yara. Tir da Gwamnan Kaduna Nasiru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *