Mahara sun kashe mutum 15 a Nasarawa
Daga Zubairu M Lawal
Wasu mahara da ba’asan ko suwayeba sun kashe mutani 15 yan kabilar Mada a kauyen Numa dake karamar Hukumar Akwanga a jihar Nasarawa.
Bayan wanan kisan gillar gungun matasa yan kabilar Mada sun gudanar da zanga zangar rashin amincewa da wanan lamarin .
Da yake jawabi na kwantar da hankalin alumman garin Akwanga Dan Majalisar Dattijai mai wakiltar mazaver Akwanga Nasarawan Eggo da Wamba ,
Sanata Philip Aruwa Ginka yayi kira ga alumman Mada da sauran Jama’a cewa kowa ya kwantar da hankalinsa .Gwamnati zata binciko wadanda suka aikata wanan laifin kuma a hukuntasu.
Ya kara da cewa yaji dadi da yadda matasa basu dauki Doka a hannu ba kuma basu farma kowa ba suka gudanar da zanga zangar lumana.
Shima a nasa jawabin Shugaban Matasan yan kabilar Mada Kyune Umaru ya dai zargi yan kabilar Fulani da ba’a ga maciji da aikata wanan ta’assar.na kisan wadanda basuji ba . kuma basu gani ba.