Kwalara ya kashe mutani 175 a sansanin gudun hijira Inji MDD

Kwalara ya kashe mutani 175 a sansanin gudun hijira

Inji MDD

Daga Zubairu T M Lawal

Hukumar kula da harkokin kiwon Lafiya ta Duniya dake qarqashin Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana asarar rayukan da ake samu a sansanin yan gudun hijira sakamakon cututuka dake addabar alumma.

Da yake magana a madadin jami’in kula da harkokin kiwon Lafiya Dakta Durkwa yace: cutar kwalara da sankaru yana illa a sansanin yan gudun hijira, ko a shekarar da ya gabata ana samu bullar cutar kwalara a sansanonin yan gudun hijirar wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutanin da dama.

Yace: kimanin mutum 11,000 suka kamu da cutar kwalarar a kananan hukumomi 28 dake yankin Arewa maso gabas inda sama da mutum 175 suka mutu.

Jihohin da abin ya faru dasu sun hada da Baron da Yobe da Adamawa, a wanan karon Hukumar kula da lafiya ta Duniya ba tayi jinkiri ba . tuni ta dauki Mata Ma’aikatan kiwon lafiya na masamman guda 454 da suke aiki na masamman wajen fadakar da alumman karkara gida gida kan abubuwan dake kawo cutar kwalara da Sankarau.

Ma’aikatan sun riqa zagawa suna shiga gidaje suna wayar dakan alumma wajen kiyaye cunkoso cikin daki guda saboda yana rige shakan iska mai amfani.

Sanan sun gargadi da a daina barin gurare cikin kazanta da zuba gurbatacen ruwa da ke kawo sauro da miyagun kwari. Sanan a rika kulawa da abinchi da za’aci da abubuwan cin abinchi.
Wadanan Ma’aikatan suna koqari sosai a yankin Arewa maso gabas, kuma anga tasirin ayyukan cikin alumma.

Durkwa ya kara da cewa; Ma’aikatan da aka dauka dukcikansu matane saboda mata suna da damar suyi cudanya da yan uwansu mata dake zaune a cikin gidajen aure sabanin namiji.

Yace; sakamakon wayar dakan alumma da wanan Bangaren ma’aikatan sukayi ya rage fargaban da muke yi kasan cewar abinda ya faru a shekarar 2018 na cutar kwalara da ya kashe mutani dayawa . abin ya tada mana hankali sosai.

Durkwa yace; an kuma qara wayar masu da kai wajen kai yara anayimasu alurarn riga kafin kwalara ko riga kafin shan’inna.

Shima da yake jawabi Babban jami’i a Ma’aikatan kiwon lafiya ta qasa, Dakta ,Christopher Ugiboko . yace Matan da aka sanyasu wanan aikin bayan tabbatar da kwarewarsu wajen harkan kiwon lafiya sai da aka qara basu horo na masamman, ta yadda zasuyi mu’amala da matan cikin gida da yadda zasu jurema kowani irin tambaya ko cin fuska.

A jihar Baron an samu mata 138 cikin 150 da aka basu horo na zagawa cikin karkara.

Shima a nasa jawabin Babban jami’in kiwon lafiya na Majalisar Dinkin Duniya Dakta Clement Peter, yace munyi farin ciki saboda canjin da aka samu a wanan karon .
Ya kara da cewa : yin amfani da wanan hanyar ya taimaka mana wajen samar da kiwon lafiya da rage cututuka dake addabar alumma dake rayuwa a Sansanonin yan gudun hijira dama karkara.

Yace; alumma sun rungumi wanan shawarwari da mata dake zagaye suka basu . kuma sunyi amfani dashi ya kuma taimakesu. Bamu samu damuwa kamar na shekarar da ta gabata ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *