Dubban yan gudun hijira sun samu sabon matsu guni a jihar Barno
Daga Zubairu M.Lawal Lafia
Bayan gobarar da aka samu wanda ya haifar da assara rayuka dana abinchi da kuma na matsugunai a kwanakin baya a sansanin yan gudun hijira. A yanzu an sabanta sabobin matsu gunan yan gudun hijira wanda ya dauki dubban jama’a da zasu zauna tare da samar da cid a shad a kuma kiwon lafiya da ma bangaren kula da koyarwa.
A shekarar bara wanan sansanin yana daukene da jama’a kimanin mutum 8,600 amma aka kara fadadashi da isashen gurin inda yanzu aka rarabashi inda zai dauki mutum kimanin 300 aka fadada sansanin ida kimanin mutum 30,000 zasu iya samu matsugunai.
A yanzu dai kimanin mutum dubu goma suke tsugunai a wanan sabon gurin . kuma ba’a bukatar a tarar da cinkoso da zai hana samar da isashen walwala da samun iska mai amfani ga alumma mazauna wanan gurin.
An kuma tsara adadin mutanin da zasu zauna a wanan sansanin da kuma abinchinsu da kuma tsaftacecen ruwansha .
Da yake jawabi a gaban dubban yan gudun hijira Malam Muhammad Goni yace; hukumar shiga da fice ta duniya ta sanya ido a kan sansanonin yan gudun hijira saboda binciko gurbatatun da suke fakewa da sunan shiga sansanin yan gudun hijira suna aikata ba dai dai ba.
Yace;yanzu dai an samu nasarar tsiratar day an gudun hijira dubu goma daga tsohon muhali zuwa sabon muhali, wanda yake da wadatace da kyawun muhali.
Shima a nasa jawabin Babban jami’in hukumar shiga da fice ta Duniya Mista Robert Odhiambo yace; hukumar shiga da fice zata kara tsaurara harkan tsaro da sanya ido a sansanonin yan gudun hijira saboda wani lokacin bata gari suna shiga sansanonin da suna suma yan gudun hijira ne kuma su haifar da mumunar abu.
Kuma a sansanonin yan gudun hijira akan koyar day an gudun hijira abubuwan da zasuyi ta fannin sana’o’I na dogaro da kai wanda zai taimakawa rayuwarsu nan gaba .
Kuma Gwamnatin jihar barno tana kara samar da matsugunan yan gudun hijiya mai rumfuna dari biyu.
Ya kara da cewa kusan mutum miliyon biyune ke rayuwa a sansanonin yan gudun hijira sakamakon matsar rikicin Boko Haram a yankunan Arewa maso gabas.
Yace; mazaunan sansanonin yan gudun hijiran akasarinsu cikin kasha tamanin matane da yara kanana. Wadanda a koyaushe suna bukatar a taimakawa rayuwarsu.
Yace; dole mu hada hannu da masu arziki wajen taimakawa wadanan alumman da suka kasance a wanan hallin rayuwarsu abin a taimaka ne. kuma akalla ana bukatar miliyoyin Dalolin Amurka domin kara agaza masu da samar masu da abubuwan jin dadi da more rayuwa da zai rika kwantar masu da hankali suji kamar suna gidajensu.
Rikicin Arewa maso gabashin Nijiriya ya jefa alumma cikin halin damuwa wasu sun rasa danginsu wasu matan sun rasa mazajensu da yaransu .