Gwamnatin Nasarawa zata hukunta duk wanda ta kama da hannu a kisan kabilar Mada Daga Zubairu .M.Lawal Gwamnatin jihar Nasarawa tad au alwashin zakulo mutanin da suka kasha wasu jama’a yan kibilar Mada a jihar Nasarawa, Cikin wanan makon ne wasu yan ta;adda da ba’asan kosuwaye ba sukayiwa alumman kabilar Mada na garin Kochu dake yankin Numa a Karamar hukumar Akwanga , kimanin mutum 16 ne aka kasha a wanan harin akasarin wadanda aka kashen matane da yara kanana. Mukaddashin Gwamnan Mista Silas Ali Agara yace; Gwamnati bazata zura ido tabari yan ta’adda na kasha jama’a babu gaira babu dalili ba. Bai kamata ace wasu da basusan darajar rai bas u kasha jama’a haka siddan . Gwamnati tad aura dammarar kamo wadanda suka aikata wanan laifin ayi masu hukunci dai dai da laifinsu. Mataimakin Gwamnan ya bayyana hakane a wajen jana’izar mamatan mutum 16 a ranar Laraba a garin Kochu. Ya kuma roki alumman wanan yankin das u kara hakuri cewan Gwamnati bataji dadin abinda ya faru ba kuma Tanana tana daukar mataki. Dan haka su kara hakuri kamar yadda sukayi a baya. Ya kuma isar da sakon ta’aziyar da Gwamnan jihar ya jajantawa alumman garin Kochu da fatan zasu baiwa jami’an tsaro hadin kai wajen gano wadanda keda hannu a wanan ta’addancin domin a hukuntasu ya zama darasi ga na baya. Shma da yake jawabi Shugaban Karamar hukumar Akwanga Honorabul Samuwel Mashi yayi godiya ga matakin da Gwamnatin jihar ta dauka na kara lamarin tsaro a wanan yanki da kuma kokarinta na tabbatar da zaman lafiya da tsare dukiyar alumman dake rayuwa a wanan gurin. |